Da kaina zan jagoranci zanga zangar tsige pantami
Wannan matar da ta sakawa kanta suna da yar fafutukar kare hakkin mutane wato Aisha yusufu tace da kanta zata jagoranci zanga zangar tsige malam pantami.
Tace a shirye take ta jagoranci zanga zangar dan ganin an tsige malamin.
Ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter.
Dama idan baku manta ba matar itace ta jagoranci zanga zangar end sars da ya faru a kwanan baya inda aka samu matsaloli da tashin hankali a kasa.
Dama tun rannan ta taba fitowa tace wannan maganar da akace malamin yayi game da yan alqaida laifi ne wanda ta kuma tabbatar da zargin da ake Masa.
Ta taba cewa ita baza ta yarda a hada mata layin wayarta da Nin number ba saboda za a iya daukar sirrinta daga karshe a kashe ta ko ayi mata wani abu.
Comments
Post a Comment