Duk wanda bashi da lambar NIN zai fuskanci daurin shekaru 14 Cewar Dr Isa Ali Pantami
Ina tabbatar muku cewa duk kan dan Najeriya da ya yi sakaci bai mallaki lambar shaidar dan kasa (NIN) ba, to zai iya fuskantar daurin shekaru goma sha hudu, kamar yadda ya ke a kundin tsarin mulkin kasar nan’’ a cewar Dr Isa Ali Pantami
Dr Isa Ali Pantami Yace ya zuwa jiya laraba talatin da daya ga watan jiya na Maris , ' yan Najeriya miliyan hamsin da daya ne suka yi rajistar lambar ta NIN . " Ina tabbatar muku cewa duk dan Najeriya da ya yi sakaci bai mallaki lambar shaidar dan kasa ( NIN ) ba , to zai iya fuskantar daurin shekaru goma sha hudu , kamar yadda ya ke a kundin tsarin mulkin kasar nan
Ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami , ya ce , duk wani dan Najeriya da ba shi da lambar shaidar zama dan kasa ( NIN ) zai iya fuskantar daurin shekaru goma sha hudu a gidan gyaran hali . Dr Isa Ali Pantami ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da kwamitin kula da sadarwa na shugaban kasa ya saba gudanarwa a duk mako .
Comments
Post a Comment