Indai zan samu wani wanda zai iya ciyar dani komai kankantarsa zan aure shi Ummi Zee Zee
Fitacciyar jarumar kannywood din nan da taci zamaninta a baya kuma yanzu ma take kan cin zamaninta wato ummi zee zee ta baiyana cewa idan harta samu wani da zai iya ciyar da ita ya shayar da ita zata aure shi duk kankantar sana'ar sa.
Jarumar a kwanan baya ta fito tace ita fa ta gaji da duniyar nan kwara ma ta kashe kanta ta huta.
To da akai bincike shine aka gano cewar wani ne ya damfareta wasu makudan kudade.
Anyi ta yamididi cewar ta mutu to amma yanzu ta fito ta nuna cewar itafa aure za tayi koda mijin da zai aureta ba wani mai dukiya bane.
Comments
Post a Comment