Ko wacce kabila tanada nata ra'ayin kuma tanada tata al'adar, dan haka koda yaushe idan wata kabilar tai wani abu sai kuga ya bada mamaki..
Kabilu kala kala ne hakama dabi'a da al'adunsu suka zama dabam dabam, wasu za kaga cikin al'adarsu basa saka kaya,haka kuma wata kabilar za kaga su matansu ne basa bari su haihu a cikin gari, wasu kuma za kuga naman mutum suke ci yayinda wata kabilar za kuga su a ruwa kawai suke iya rayuwarsu.
Kabilar da basa binne gawar mutum idan ya mutu
Yau muna dauke muku da wata kabila mai abin mamaki wacce su basu da damuwa da zarar sunyi bako to suna mallakawa bakon matarsu ne ya kwana da ita su kuma su kwana a wani dakin dabam.
Sannan bayan haka su a al'adarsu mace bata da ikon zaben wanda zata aura dole mahaifinta ne zai zaba mata koda bata sonsa dole tayi hakuri ta zauna.
Amma duk da haka koda yau matar ta tare a gidan sai akai bako tofa saidai bakon ya kwana da matar shi kuma mijin ya koma ya hakura ya kwana a wani dakin.
Sunan wannan kabilar ova Himba kuma suna zaune ne a kasar Nambia.
Matan wannan kabilar basu da wani zabi ko aikata wani abu dole sai mijinsu ya amince amma duk da haka in sun so zasu iya kin kwana da mijinsu suje can su kwana da wani da yazo musu ziyara.
Comments
Post a Comment