Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokaci ya gida ya aiki kuma ya ibada Allah ya taimaka mana.
Cikin shirinmu na zagaya Duniya yau muna tafe muku da jerin wasu kasashe wanda suke da matukar yawan mutane inda kasa ta bakwai daga cikinsu ta bada mamaki.
Bazanje daku nesa sosai ba amma dai kunsan munada kasashe masu yawa a Duniya wasu kasashen manya ne sunada girman kasa amma basu da hawan mutane yayinda wasu keda tarin mutane amma basu da girman kasa sannan akwai kasashe masu girman kasa tare da tarin mutane.
Yau Insha Allahu zamu kawo muku jerin kasashe goma wanda suka fi yawan mutane a Duniya.
√ kasar mexico itace kasa ta goma a tarin mutane domin tanada mutane kimanin milliyan 120
√ kasar Russia itace kasa ta tara wadda take dauke da mutane miliyan 146
√ Bangladesh itace kasa ta takwas a jerin kasashe masu yawan mutane domin tanada yawan mutane miliyan 167
√ Nijeriya itace kasa ta bakwai da take da tarin al'umma miliyan 202
√ Brazil kasar brazil itace ta shida tanada mutane miliyan 211
√ Pakistan tana jerin ta biyar tanada mutane masu yawa da suka kai miliyan 216
√ Indonesia itace ta hudu tanada mutane miliyan 270
√ United States ita ta zama ta uku da adadin mutane miliyan 329
√ sai kasar India wacce ta zamto ta biyu tanada mutane biliyan 1.37
√ China itace ta farko wajen tarin mutane a Duniya itace kasar da tafi kowacce kasa yawan mutane tanada mutane kimanin billiyan 1.43
Comments
Post a Comment