Kayan abinci na yin tashin goron zabi a cikin wannan watan
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya Ya Zarce Kashi goma sha takwas
Hukumar kula da kididdiga a Nijeriya ta sanar da samun hauhawar farashin kayayyaki a watan Maris wanda ya kai kashi 18.17 sakamakon tashin farashin kayan abinci da aka gani.
Wannan sabon adadin ya zarce wanda aka gani a watan Fabarairu wanda ya kai kashi 17.33, kuma daga cikin alkaluman da hukumar ta gabatar ya nuna cewar an samu karin farashin abinci da ya kai kashi 22.95 sabanin wanda aka gani a watan Fabarairu na 21.79.
Masana tattalin arziki na danganta hauhawar farashin da tsadar rayuwa da kuma matsalolin da Najeriya ke fuskanta na rashin tsaro dake hana manoma zuwa gonakin su.
Alkaluman hukumar sun ce an fi samun hauhawan farashin a Jihohin Rivers da Niger da kuma Gombe, yayin da aka samu akasin haka a Jihohin Zamfara da Yobe da kuma Kebbi.
Comments
Post a Comment