Min menu

Pages

Kuna da masaniyar mutane sama da dubu dari biyar ne suka musulunta a hannun Dr Zakir Naik

Kuna da masaniyar mutane sama da dubu dari biyar ne suka musulunta a hannun Dr Zakir Naik




An cafke wani mahaifi yana lalata da yarsa

Fitaccen malamin nan Dr. Zakir Abdulkarim Naik ya haddace Al-Qur'ani yaruka da dama domin ya haddace shi da Larabci, ya haddace shi da Indiyanci, ya haddace shi da yaren Urdu, sannan kuma ya haddace shi da Turanci.


A shekarar 1991 ne Dr. Zakir Naik ya fara aikin Da'awa, wato kira zuwa ga addinin Allah (S.W.T) inda ya kafa cibiyarsa ta Islamic Research Foundation, wacce ɗan'uwansa Muhammad Naik yake jagorantar ɓangaren Maza, da kuma ɓangaren mata inda matarsa Dr. Farhat Naik ke jagoranta.


Wannan cibiya ta Dr. Zakir Abdulkarim Naik ta shahara a ƙasar Indiya da ma nahiyar Turai wajen yin kira tare da yaɗa addinin Musulunci ta hanyar amfani da hanyoyin kimiyyar zamani irin su Settilite, T.V Channels, Cable T.V, Networks da sauransu. Haka kuma wannan cibiya tasa tan da ƙwararun masu wa'azi Maza da Mata da suka haɗa da shi kansa Dr. Zakir Naik, Yasir Qadhi, Faizur Rahman, Sheikh Sanaullahi Madani, Husain Ye, Yusuf Estes, James Yee da Suraj Wahhaj, da kuma Shugabar Mata Dr. Farhat Naik.


Haka kuma akwai shahararrun Malamai waɗanda suke taimakawa wannan cibiya a wasu lokatan waɗanda suka haɗa da; Dr. Israr Ahmad da Salman Husain Nadwi da sauransu. Babbar manufar wannan cibiya shine yaɗa saƙon Musulunci ta hanyar kiran waɗanda ba Musulmai ba zuwa ga addinin Musulunci ba tare da faɗa ko kuma rigima ba. Wanda hakan ne yasa a ƙarƙashin wannan cibiya sama da Mutane 500,000 suka musulunta daga shekarar 1991 zuwa 2020.


Dr. Zakir Naik ya shahara matuƙa a duniya saboda ƙwarewarsa wajen tattaunawa ta ruwan sanyi tare da iya gabatar da wa'azi da kuma tattunawa da shahararrun Kiristoci. Mafi shahararar tattaunawar da ya yi ita ce tattaunawa da William Campbell a shekarar 2000 a Chicago ta ƙasar Amurka mai taken: The Quran And The Bible In The Light Of Science, wato Qur'ani Da Injila A Hasken Kimiyya. Sannan kuma a ranar 21 ga Janairu, 2006, Dr. Naik ya yi tattaunawa da Sri Sri Ravia Shankar a Bangalore mai taken: God In Islam and Hindusm. Watau Matsayin Ubangiji A Addinin Musulunci Da Addinin Hindu.


An ruwaito cewa daga watan Satumbar 2000 zuwa watan Yulin 2002, Dr. Zakir ya Musuluntar da Amurkawa har kimanin Mutum 34,000, banda al'ummar ƙasar sa ta India waɗanda koda yaushe suke ƙara fahimtar addinin Musulunci a dalilin sa.


Dr. Zakir ya ziyarci ƙasashen duniya masu tarin yawa inda ya gabatar da lakcoci da tattaunawa. A shekara 2010 ne aka hana shi shiga ƙasar England da ƙasar Canada bayan an shirya taro wanda zai gabatar da lakca a can, inda Ministan Harkokin Cikin Gida Ta England, wato Theresa May ta bayyana rashin amincewa da shi.


An kuma sake hana shi shiga Canada bayan da Tarek Fatah, Shugaban cibiyar Muslim Canada Congress ya gayyace shi. (Controversial Muslim Televangelist, Zakir Naik Banned From Toronto Conference. Kathryn Blaze Carlson. Norwalk Post 22 June, 2010).


Dr. Zakir ya zama shahararre a duniya saboda jajircewar sa wajen kira da kuma yaɗa addinin Musulunci. Wanda hakan yasa ya ringa fuskantar tsana da tsangwama musamman daga ƙasar sa ta India, wanda a dalilin takunkumi da ƙasar ta India ta sa masa yayi hijira zuwa ƙasar Malaysia.


To muna roƙon Allah (S.W.T) Ya cigaba da yi masa jagoranci, Ya kuma ƙaro mana ire-irensa masu yawa waɗanda zasu sadaukar da komai nasu domin yaɗa addinin musuluncitare da kare shi a ko'ina. Amin.

Comments