Mutane da dama na ci gaba da gudun neman mafaka a Jihar Taraba
Al'umma a Ƙauyen Dogongawa dake Karamar Hukumar Takum a Jihar Taraba na ci gaba sa tserewa biyo bayan wani hari ta'addanci a shekaran Jiya Juma'a.
Mutane sama da dubu biyu ne suka gudu suka bar muhallin su, yayin da wasu da dama suka yi batan dabo ba a san inda suka yi ba.
Wani Mazaunin Kauyen mai suna James Orya ya tabbatar da Wannan lamari wa manema labarai inda ya ce gidaje da dama ne aka kona kurmus yayin da aka daidaita bishiyoyin amfanin gona.
"Akwai wasu manyan hanyoyi da suka biyo ta kauyen wadanda sun taso ne daga garin Takum zuwa Katsina-Ala kuma Kullum motoci na wucewa ba dare ba rana, to amma bakon al'amari da muka gani shine yadda wasu manyan motoci suka zo suka fara bude mana wuta" a cewar shi.
"Mutane sama da dubu biyu ne suka tsere a wannan yanki, kuma yawancin su suna neman mafaka ne a Jihar Binuwe dake makotaka da mu".
A yanzu haka dai wannan al'amari na ci gaba da tada hankalin jama'a ciki ht da na gwamnati don ganin an dakile shi.
Comments
Post a Comment