Min menu

Pages

Shin kunsan wani yanki a Duniya da rana tana faduwa minti 40 take sake fitowa?

 Ko kunsan wani yanki a Duniya wanda da zarar rana ta fadi bata wuce minti 40 take sake fitowa?



Duniya nada matukar girma kuma tanada fadi wanda hakan yasa aka samu yankuna masu yawa.


Yau munzo muku ne da sunan wani yanki wanda da zarar rana ta fadi take sake fitowa bayan yan mintuna.


Karanta:- wani gari wanda idan dare yayi gari baya wayewa sai yayi wata biyu


A Duniya akwai wani gari da rana take faduwa tsakiyar dare wato 12:43am ta sake fitowa bayan minti 40 kuma wannan irin daren yana faruwa ne a cikin wata 2 da rabi, wannan ne yasa ake kiranta da kasa mai rana tsakiyar dare.


Wannan abun yana faruwa ne a garin #HammerFest na kasar Norway, haka ma kasar Norway kasa ce fitacciya mai dauke da ababe na ban sha'awa wadda hakan yake janyo mata masu yawon buda idanu a kowanne lokaci.


Kasar Norway kasace mai arziki a duniya kuma take da kyakkyawun abubuwa na burgewa, kuma kasar ta zaunu ne a wani sashe da ake kira da Arctic Cycle wato wani layi dake kusurwar duniya ta Arewa.


Wannan Fitowar Rana na tsakiyar Dare yana faruwa ne cikin kwana 76 tsakanin watan May da July a kowacce shekara.


Hammerfest Kyakkyawan Wuri ne wanda alummar wurin ke rayuwa mai kyau cikin koshin lafiya. 


Jama'a da dama na zuwa wurin daga wurare masu nisa domin ganin wannan wurin mai cike da ikon Allah.

Comments