Shugabannin kasashen da sukayi zaman gidan yari bayan sun gama mulkin kasar su saboda mummunan aikin da suka aikata
Nahiyar afrika yanki ne dake cike da gurbatattun shugabanni masu cin hanci da kuma rashawa a mulkin su, da wuya kaga shugaba a afrika yayi mulki ya gama ba tare da ya aikata wani gagarumin aiki marar dadi ba walau yin gaba da dukiyar kasa ko kuma aikata wani laifi ba.
Koda yake wasu sun ciri tuta domin sun gabatar da shugabancin su ba tare da sunyi sata ko sun tauye hakkin talakawan da suke shugabanta ba.
To yau dai cikin ikon Allah zamu kawo muku sunan wasu shugabannin kasashe da sukayi mulki amma daga karshe sai suka karashe sauran rayuwarsu a gidan yari saboda sun aikata laifuka masu yawa.
Alphonse Massamba Debat
Shine tsohon shugaban kasar Congo brazzaville yayi mulkin shugabancin kasa a shekarar 1959.
Ya gabatar da mulkinsa cikin rashin adalci da kyautatawa, wannan yasa aka sauke shi da karfi akan shugabancin a shekarar 1968 sannan aka kamashi kuma aka kulle shi.
Cannan banana
Shine shugaba na farko wanda aka zabe shi yin shugabancin kasar Zimbabwe, a kalla yayi shekara bakwai yana mulki hakan yasa aka kamashi da aikata manyan laifuka har wajen guda goma sha daya wanda a karshe shima aka kamashi sannan aka turashi gidan yari.
Gyude Bryant
Shekara uku yayi yana rike da wani babban mukami a kasar Liberia daga karshe shima an kamashi saboda yaki halartar kotu saboda wani abu da ake zarginsa dashi.
Pasteur bizimungu
Shine shugaban kasar Rwanda na uku domin ya zamto shugaban kasar ne a shekarar 1994 wanda yaci gaba da mulki har zuwa shekarar 2000.
Shima dai an daure shi saboda shigo da wata doka da yayi wanda aka hanata a shugabancin kasar Rwandan tsawon lokaci.
Wadannan sune kadan daga cikin mutanen da aka kamasu bayan sunyi mulki to amma ya kuke gani a nijeriya ko za'a samu irin wadannan shugaban nin?
Comments
Post a Comment