Wata kabila wacce basa yadda su binne gawar dan uwansu idan ya mutu saboda wani dalili nasu.
Gwamnan Zamfara ya sauke wani hakimi daga mukaminsa saboda zarginsa da laifin yiwa yan bindinga aiki
Kabilu dai kala kala ne a duniya kuma kusan tsarin ko wacce kabila yasha bamban dana wata kabila, hakan yasa da wuya ku samu kabila wacce suke al'ada iri daya dana wata kabilar.
Wasu hanyoyi da mai azumi zai bi domin maganin yunwa
Yau cikin wannan gidan munzo muku da tarihin wata kabila wacce basa binne mamaci idan ya mutu saboda wani abu irin nasu.
Kabilar maasai wata kabila ce da kusan suke rayuwa a jeji inda aka fi samunsu a kasar Kenya dake arewacin kasar Tanzania a Nahiyar Afrika.
Kabilar na daya daga cikin kabilu masu yawan al'umma da yalwar mutane.
Kabilar maasai sunada wani tunani nasu akan matattu musamman saboda yawan mace mace da suke samu a cikin kabilar tasu, musamman mutuwar yara kanana saboda wata cuta da suka danganta ta da kabilar tasu.
Wannan yasa koda sun haihu basa wani saka rai da jaririn da suka haifa har sai sunga ya haura shekara uku da wata uku daga nan za suyi masa bikin suna.
Duk mutanen da suka mutu cikin kabilar basa binne su saidai su saka musu wani sinadari su kawar dashi gefe domin sunce binne gawa na karawa kasar cuta.
Wani lokacin idan mutum ya mutu suna shafe shi da jini da kuma kitse kafin daga baya su saka masa magani.
Dan haka binne mutum a wannan kabilar nada matukar wahala ga tarin tsada.
Comments
Post a Comment