Wadannan sune jarumai a musulunci
1- Jarumi shine saiyidna Uthman a lokacin da ya karance gabaki daya kur'ani a raka'a daya.
2- Jarumi shine Imam Ali a lokacin da ya karya kofan Khaibar shi kadai.
3- Jarumi shine Zabair bn Awwam a lokacin da yayi diran mikiya akan ganuwar kafirai domin ya bude kofar nasara ga musulmai.
4- Jarumi shine Darraru bn Azwar a lokacin da ya fuskanci rundunar Romawa shi kadai.
5- Jarumi shine Khalid bn Walid a lokacin da ya dira tsakiyan kafirai ya kashe shugabansu kuma ya dawo cikin tawagarsa a cikin aminci.
6- Jarumi shine Umar bn Abdulazeez, da yayi kusan shekara biyu ya neman wanda zai bawa zakkah amma bai samu ba(sabida adalcinsa kowa a wadace yake).
7- Jarumi shine Khalid bn Walid da ya gwabza yaki 100 amma baiyi rashin nasara ko daya ba.
8- Jarumi shine Imam Aliyu da yayi yaki da takobi biyu kuma yana sarrafa dokinsa da kafafunsa.
9- Jarumi shine Imam Ja'afar da yake rungume da tutar musulunci bayan an datse hannayansa.
10- Jarumi shine Saiyidna Umar a lokacin da musulmi ke san`da zuwa madina, shi kuwa ya dauki takobinsa, ya sanya bakansa a kafadarsa. Ya tafi dakin Allah inda yayi dawafi har guda bakwai sannan ya tsaya a Maqamu Ibrahim, yayi sallah raka'a biyu. Sai ya kalli dandazon kafirai yace dasu "Wanda ke son uwarsa tayi wabi, dansa ya zamo maraya, matarsa ta zamo bazawara, toh ya hadu dani a bayan wannan tsauni". Kuma babu wanda ya iya ya bisa.
11-Jarumi shine Saiyidna Hamza a lokacin da yaji labarin cewa Abu Jahal ya fada wa ma'aiki s.a.w bakar magana kuma ya cutar dashi, sai ya tinkari Abu jahil cikin fushi yace dashi 'Shin zaka cutar dashi alhalin ina kan addininsa, ina fadar duk abunda yake fada!.
Comments
Post a Comment