Min menu

Pages

Annobar korona:- Yan kasar India sun saduda suna sassare gumakan da suke bautawa

 Bayan Korona ta kashe dubban mutane, yanzu haka yan Indiya na ta Sassare Gumakansu




A yanzu haka dai kiyasi a kasar Indiya na nuni da cewa mutane sama da dubu dari biyu ne suka gamu da ajalinsu sakamakon cutar nan da ta addabi duniya a chan baya wato Korona ko kuma Covid-19 kamar yadda aka fi sani.


Adadi mafi muni da ya ritsa da kasar shine Na yan baya-bayan nan da mutane sama da dubu hudu suka hallaka a shekaran Jiya Alhamis kawai.


Baya ga wadannan mace-mace kuma, kasar a yanzu haka tana da wasu karin mutane dama da miliyan ashirin da Korona ta yi ram da su.


Ko da yake kasar ita ta fi ko wace kasa a fadin duniya sarrafawa tare da amfani da allurar rigafin cutar, amma hakan bai hana ta shiga halin ha'ula'i ba, lamarin da wasu ke dangantawa da rashin bin Ka'idojin da aka gindaya na cutar.


Kasar ta Indiya wacce mafiya akasarin al'ummar ta mabiya addinin Hindu ne dake bautar gumaka, a yanzu haka a iya cewa kan mage ya fara wayewa tare da daukar haske inda suka fara gane cewa lallai babu wani Sarki sai Allah.


Cikin wani faifan bidiyo da ya yi ta balaguro a shafukan sada zumunta na zamani, an ga yadda wasu mata daga kasar ke sassare ababen bautar nasu, tare da kalaman cewa "kun bamu kunya", ba mu san haka kuke ba"


To da ma dai a kulli yaumin ana hango al'ummar ta hindu na durkusa wa gumakan nasu suna neman mafita dangane abubuwa da suka shafe ciki har da ita kanta citar Korona, duk da irin kiraye-kirayen da Mallaman addini ke yi na a koma ga Allah.


A yanzu haka za mu iya cewa wata kila Allah ne Ya aiko wa wadannan mutane kadan daga cikin ikonSa don nuna wa duniya izinar cewa babu wani mai yi bayan Shi.

Comments