Min menu

Pages

Ba Janar Attahiru ne na farkon shugaban sojojin daya mutu a hatsarin jirgi ba shine na hudu ga sunan sauran da suka mutu

 Ba Janar Attahiru ne na farkon shugaban sojojin daya mutu a hatsarin jirgi ba shine na hudu ga sunan sauran da suka mutu..



Ashe ba Janar Attahiru bane ya fara mutumuwa a hatsarin jirgi ba cikin manyan sojojin kasar nan, kafin shi akwai mutane uku.


Hakika mutuwar shugaban sojojin Nigeria Ibrahim Attahiru tayi matukar girgiza mutanen kasar biyo bayan kyautata zato da ake yi masa na yaki da yake da yan ta'adda da sauran masu tada kayar baya a Nijeriya.


Mutane sunyi jimamin rashin gwarzon jarumi na sojoji.

Wasu na tunanin kamar shine shugaban sojojin Nigeria na farko daya taba yin hatsari cikin jirgi harya mutu.

To saidai bashi kadai bane cikin manyan sojojin ko kuma shugabannin sojojin Nigeria da suka mutu a hatsarin jirgi dan kafin shi akwai mutane uku wanda shugabannin sojoji ne da suka mutu a hatsarin jirgin.

Dan haka ga jerin sauran mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin


JOSEPH AKAHAN

Shima wani jami'in soja ne da ya rike mukamin shugaban sojojin Nigeria a shekarar 1967 kuma shima ya mutu ne a hatsarin jirgin akan hanyar sa ta komawa gida domin ya huta saboda halartar wani abu da yaje.



SHITTU ALAO

Ya mutu ne yana shekara 32 wanda duka shekarar sa biyu yana rike da mukamin shugaban sojojin Nigeria.

An nuna kusan shine jami'i na farko daya rike mukamin shugaban sojoji yana matashi.

Shima ya mutu ne a hatsarin jirgin lokacin da aka samu matsala ta yanayi da kuma wata matsalar hakan yasa matukin jirgin yai saukar gaggawa to saidai an samu matsala ya fada kan bishiya inda hakan ya jawa jirgin yin hatsari.



ANDREW AZAZI

Shi wannan ba kamar sauran yake ba shi ya mutu ne jim kadan bayan bayan yabar aiki to amma dai shine shugaban sojojin da aka zaba a shekarar 2006 lokacin mulkin obasanjo.

To shima dai in kuka bibiyi tarishi jirgin ne ya zama ajalinsa.





Comments