ZA A RAGE ALBASHIN MA'AIKATAN GWAMNATIN TARAYYA —MINISTA
Shugaba Buhari ya ba da umarnin rage albashin ma’aikatan wasu hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya.
Ministar Kudi, Zainab Ahmad ta ce umarnin na Buhari zai rage yawan kudaden da take kashewa wajen gudanar da gwamnati.
“Shugaban Kasa ya umarci Kwamitin Tsara Albashi, wanda nake jagoranta, tare da Shugabar Ma’aikatan Tarayya da sauran ’yan kwamitin, cewa mu sake nazarin albashin ma’aikatun domin rage kudaden,’’ inji ta.
Ta bayyana hakan ne a jawabinta ga taron da aka yi kan rage kashe kudaden gudanar da gwamnati wanda Hukumar Yaki da Zamba da Dangoginsa (ICPC) ta shirya a Abuja ranar Talata.
Minsitar ta ce Gwamnatin za ta kuma soke wasu kudade marasa ma’ana da ke kunshe a cikin kasafin shekara na ma’aikatun gwamnati.
Yawancin hukumomin gwamnati kan sanya kudaden sayen motocin aiki da kwamfutoci da sauransu a kasafinsu na kusan duk shekara.
Ministar ta ce, “Kasafin kudin kasar nan cike yake da tanadin kudaden ayyukan wasu yawan maimaitawa kuma hakan bai dace su.”
Da yake bayani a wurin taro, Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya ce matsalar ma’aikatan bogi a ma’aikatu na daga cikin matsalolin da ke sa albashin wuce misali.
A cewarsa, muddin aka kakkabe ma’aikatan bogi, to za a samu saukin abin da ake kashewa wurin biyan albashi.
Comments
Post a Comment