Dana kashe kaina da yanzu malamai sun hau mumbari sunata yamididi dani amma lokacinda nace zan kashe kaina babu wanda ya kirani yai min nasiha Ummi zee zee.
Malaman nan sai a hankali, lokacinda nace zan kashe kaina cikinsu babu wanda ya kirani yai min nasiha amma da na kashe kan nawa na tabbata da yanzu duk mumbarin da suka hau sai sun kalubalance ni wasu ma sun tsine min inji Ummi zee zee.
Tsohuwar jarumar wasan hausa wadda tauraruwar ta ta haska a baya ta koka a cewarta yadda malamai sukai shiru ba tare da sunce komai ba lokacinda ta yanke kudurin zata kashe kanta tace babu wani daga cikin malaman da yayi mata nasiha ya nusar da ita rashin kyawun hakan kuma da ta yanke hukuncin a lokacin ta kashe kan nata da an cika kafafen yada zumunta da maganganu a kanta.
Ko kwanan baya jarumar ta baiyana cewa arna sunfi musulmi tausayi lokacinda wani ya damfareta wasu makudan kudade.
Tace babu wani da ya tayata jimami daga karshe ma dariya aka dinga yi mata wasu ma har murna da fada mata maganganu suke.
Comments
Post a Comment