Min menu

Pages

Dole ne a tsige Buhari saboda wannan dalilin

 Dole ne a tsige Buhari<><>Cewar Ƙungiyar Dattawan Arewa



Kakakin Ƙungiyar dattawan Arewa Hakeem Baba-Ahmad ya bukaci majalisar dokokin tarayya da su tsige Shugaban Kasa Muhammadu Buhari muddin ya gaza taɓuka abin arziki wa kasar nan musamman bangren tsaro.


A yan baya-bayan nan dai shugaban Buhari na fuskantar matsin lamba daga bangarori daban-daban bisa irin yadda matsalar tsaro ke kara yi wa kasar dabaibayi.


Da yake magana a wani shirin Talabijin na AIT, Baba-Ahmad ya ja hankalin masu rike da madafun iko da su yi abinda ya dace wa kasar nan ba wai babatu da alkawarorin karya ba.


"Wato zabi daya da muke da shi a kasar nan shine, ya kamata yan majalisa su dubi menene gwamnati ta yi, nasarori da kuma akasin haka, sai su dauki matakin da doka ta ce, kan cewa dole ne a kare ran ko wane dan kasa".


"Idan Buhari ya gaza yin haka, to dole ne a tsige shi, a yan watanni shida da suka gabata, Shekara biyu menene Shugaban Kasar ya yi na kare yan kasar nan? Magana ta gaskiya babu, kuma kun zura idanu Abubuwa suna ta rinchabewa" Cewar Hakeem.


Ya kara da cewa zabi na biyu kuma ya rage wa yan ƙasa ne su hada kai su abinda ya dace domin su ake mulka.


Wannan maganganu na Baba-Ahmad na zuwa ne yan kwanaki bayan da fadar shugaban kasa ta yi sanarwar cewa akwai waɗansu shugabanni dake kitsa yiwa gwamnati juyin mulki.

Comments