Idan mutum yayi sata a wannan garin to hukuncin da ake masa shine a yanke masa hancinsa da fuskarsa a barshi shine hukuncin.
Kowa dai ya sani duk wani barawo ko kuma wanda ya dauki kayan wani idan har an kamashi to ana yi masa hukunci daidai da laifin da yayi a cikin ko wacce al'umma ne.
Wasu idan sun kama barawo to za kuga dukansa kawai suke wasu kuma suna yanke masa hannu ne, yayinda a wani garin kuma idan suka kama barawo to kuwa shikenan shi domin kashe shi za suyi, wasu suna sakawa barawon taya ne su kone shi wasu kuma da duka kurum zasu kashe mutum.
Yau muna dauke muku ne da sunan wani gari dake can yankin wanda su idan suka kama barawo hancinsa kawai zasu cire sannan su yanki wani guri a fuskar barawon kamar su cire lebe ko kunne.
Rhinocolura shine sunan gurin da ake wannan hukuncin kuma gurin yana nan a kasar Egypt.
Mutumin daya gina wannan wurin wani sarki ne daga sarakunan Egypt din inda yayi hakan ne domin horas da barayi masu sata.
Duk kan mutanen dake wurin suna rayuwa duk barayi ne domin sun taba yin sata.
Dan haka duk zakuga bakinsu da hancinsu a cire.
Wannan yasa mutanen basa shiga cikin al'umma ko suce zasu gudu domin kowa ya gansu yasan barayi ne dan haka suka tsaya suna rayuwarsu anan.
Comments
Post a Comment