ALLAHU AKBAR: Karanta jawabin da margayi Shugaban Sojojin Nigeria Laftanar Janar Ibrahim Attahiru yayi ana saura kwana 2 ya rasu
A ranar Laraba 19 ga watan Mayu 2021 (yau kwana Uku kenan) Shugaban hafsan sojin Nigeria, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya bayyana cewa ya san akwai kalubale da dama da ke tattare da sha'anin tsaron kasarnan amma dai shi ya lashi takobin zai kawo sauye-sauye sosai a fasalin sojin kasarnan da kuma yaki da ta'addancin da yayi wa Nigeria katutu duk da kalubalen da yasan zai fuskanta.
Wata jarida ta ruwaito margayin wanda ke jawabi a wajen taron horas da manyan soji da akayi a 2 Division auditorium, Adekunle Fajuyi Cantonment, a Ibadan, ya ce yasan akwai kalubale da dama amma ya daura damarar kawo sauyin da sojoji da yan kasa zasu ji dadinsa.
Kuma ya ce zai inganta dabarun yaki da ake amfani dasu a baya wajen kokarin kawar da rashin tsaro a kasarnan ta hanyar koyawa sojoji sabbin dabaru da turasu karo ilimi da dabarun yaki daidai da zamani da kuma kula da hakkokinsu da uwa uba sama masu kayan aiki. Ya hori manyan sojin da su dai su kasance masu amana da son kasa da kishin ta da jajurcewa domin akai gaci.
ALLAHU AKBAR yana ta shirya tsari ashe kwana Biyu ya rage masa! Yayi magana ranar Laraba yau Juma'a ya mutu a hadarin jirgin sama a kusa da filin jiragen sama na Kaduna ya zo wani aiki.
Ance cikin wadanda ke tare dashi a cikin jirgin sun hada da:-
1. LT GEN I ATTAHIRU.
2. BRIG GEN MI ABDULKADIR.
3. BRIG GEN OLAYINKA.
4. BRIG GEN KULIYA.
5. MAJ LA HAYAT.
6. MAJ HAMZA.
7. SGT UMAR.
MATUKA JIRGIN SU NE:-
8. FLT LT TO ASANIYI.
9. FLT LT AA OLUFADE.
10. SGT ADESINA.
11. ACM OYEDEPO.
Dukkaninsu babu wanda ya tsira da ransa a hadarin jirgin wanda ya faru da misalin karfe 6 na yamma agogon Nigeria ranar Juma'a 21/05/2021. Tuni anyi Jana'izar su.
Comments
Post a Comment