DA DUMI-DUMIN SU!
Kungiyar Hamas ta Palasdiwa ta mayar da martani ta harba rokoki a cikin kasar Isra'ila
Yanzu haka kungiyar Hamas mai kokarin kare Palasdiwa daga hare-haren ta'addanci ta mayarda martani kan hare-haren da kasar Isra'ila take kaiwa Palasdiwa musulmai masu gudanar da ibada a masallacin Kudus.
Kungiyar dai yanzu haka tana ci gaba da harba rokoki a cikin kasar Isra'ila tun da sanyin safiyar yau Talata. Kuma kawo yanzu an tabbatar da mutuwar Yahudawa 10.
Kungiyar ta bayyana cewa babu dalilin da zai sa ta zura ido kan kasar Isra'ila mai kokarin mamaye masallacin Kudus.
Saboda haka kungiyar ta bayyana cewa babu gudu babu ja da baya zasu ci gaba da harba rokoki a cikin kasar Isra'ila har lokacin da jami'an tsaron kasar suka janye daga masallaci mai tsarki na Kudus.
Shin a ganin ku ko wannan mataki da kungiyar Hamas ta dauka ya yi daidai?
Comments
Post a Comment