Wasu na ganin mutuwar shugaban sojojin Ibrahim Attahiru bata rasa nasaba da wannan dalilin
Bazai ma amsa sunan Mumini ba, idan mutum bai imani da kaddara mai kyau da marar kyau daga Allah suke ba, amma babu laifi dan mutum yayi zargi akan sababin abkuwar kaddarar.
Bafa sabon Al'amari bane, wasu daga jami'ai su kitsa makirci ko su kashe wani jami'in da ya samu wata falala akansu, ko ya samu wani mukami akansu a Nigeria, saboda maslahar Kabilanci, ko kuma yanki, Kisan Sardauna da kuma Tafawa Balewa ya ishi su zamo izina akan haka.
Lallai gaskiya ne ta karkashin kasa akwai wadanda basu son gushewar matsalar tsaro a Nigeria, kamar yadda idan akace za'a rufe kasuwanni yan kasuwa zasubi ta duk hanyar da zasu iya domin dakile faruwar hakan, haka zalika suma a duk sadda suka fuskanci wani ya himmatu da kawo karshen matsalar tsaro a Nigeria, to zasu iya bi ta duk hanyar da zasu iya bi domin ganin sun dakile shi, inaga ba mamaki shi yasa Burtai yace "Matsalar tsaro sai ta zarce shekaru 20 a kasarnan".
Kanar Abu Ali, ya samu daukaka cikin kankanin lokaci tare da samun mukamai bayan zamowar sa gwarzo kuma jajircecce marar tsoro kuma mai kananan shekaru, menene ya zamo karshen sa, to nasane kawai ya bayyana akwai dubun sa da aka kwantar kasa wadanda Duniya bataji labarin su ba.
Har yau, akwai masu kyautata zargin cewa "Mutuwar Sarkin Musulmi maciddo, da Senator Sule yaro Gandi a jirgin sama wani shiryayyen al'amari ne, da akayi rufa-rufa akansa saboda sunki amincewa tsarin tazarce".
Sau nawa jami'ai suna fitowa suna boye sunayen su a gidajen Redio suna bayyana irin makircin da akeyi ta karkashin kasa a game da matsalar tsaro..?
Ka duba kasar Chad, karfin sojinta bai kai rabin-rabin na Nigeria ba, shin me yasa sukaci karfin Yan Ta'adda a kasarsu, amma mu namu sai kara fadada sukeyi duk da makudan kudaden da ake kashewa..?
ALLAH YA BAMU ZAMAN LAFIYA.
ALHAMDULILLAH.
Comments
Post a Comment