WATA AL'ADA:- wacce mutum zai dauki azumi idan ya fara tsufa har ya mutu
Kamar yadda kuka sani kowacce kabila suna da al'adarsu wacce suka gada iyaye da kakanni dan haka suke aikata wannan al'adar suma.
Wasu al'adar da suke ta sabawa addini koda yake mafiya yawan masu aikata al'adar ma da yawa ba musulmi bane.
Akwai addinai da dama da suke yin azumi a matsayin ibada koda yake mu musulmai mune muka tabbatar da haka domin addininmu na gaskiya ne kuma an sanar da yin azumi cikin litattafai.
Amma duk da haka wasu addinan ma suna gabatar da nasu azumin to saidai yasha bamban da irin namu domin su nasu babu ka'ida ko kadan a cikinsa.
Dan haka yau nake tafe muku da tarihin wata kabila dake can kasar India inda suka sanya dokar yin azumi har mutuwa ga duk wani mutum daya fara tsufa.
Sunyi imanin cewa duk mutumin daya mutu za a dake haifo shi ya dawo dan haka da zarar mutum ya tsufa to daga lokacin zai dauki azumi wanda bazai daina ba har sai ya mutu.
Wannan al'amarin wata kotu ce a kasar ta sanar da yanke wannan hukuncin duk da wasu da dama na neman a soke wannan dokar.
Sunan wannan al'adar ta azumin santhara, wanda wasu daga cikin mabiya addinin Hindu suke gabatarwa.
Sune suka riki wannan al'adar ta yin azumi ko daina cin abinci da zarar mutum ya fara tsufa ko rashin lafiya mai tsanani ta kama shi.
Ku kalli bayanin kadan daga cikin irin al'adar a kasa
Comments
Post a Comment