Za Mu Cigaba Da Biyan Sabon Tsarin Albashi Ga Ma'aikatan Jihar Jigawa, Komai Tsananin Matsin Tattalin Arziki
Gwamnatin jihar Jigawa ta bada tabbacin cigaba da biyan sabon tsarin albashi da fansho da kuma sauran hakkokin maaikata koma tsananin matsin tattalin arziki.
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bada tabbacin hakan a jiya Asabar lokacin bikin ranar ma'aikata ta bana da aka gudanar a dakin taro na Sir Ahmadu Bello dake Dutse.
Gwamna Badaru Abubakar, ya ce duk da matsain tattalin arziki da gwamnatoci suke fuskanta a kasa da duniya , gwamnatin jiha tayi kyakkywan tanadin katta kwana domin ganin ba a samu matsala ba wajen biyan albashi da sauran hakkokin maaikata.
Gwamna Badaru ya kara da cewar gwamnati za ta cigaba da tallafawa kananan hukumomi domin ganin suna biyan albashi akan lokaci inda yace koda a watan jiya sai da gwamnatin jiha ta cikawa kananan hukumomi miliyan 418 domin biyan albashin ma'aikata.
Daga nan ya bukaci maaikata da sauran alummar jihar nan su dage da yin adduoi domin magance kalubalen tsaro da kuma matsin tattalin arziki dake damun kasar nan.
Tun farko a nasa jawabin shugaban kungiyar kwadago ta jiha Comrade Sanusi Alhassan Maigatari ya yabawa gwamnatin jiha saboda biyan albashi da fansho akan lokaci duk da matsalar tattalin arziki da ake fuskanta, Comrade Sunusi Alhassan yace kungiyar tana alfahari da yadda gwamnatin jiha take biyan albashi da fansho duk kuwa da halin matsin kudaen da ake fama da shi.
Ya ce ma'aikata na daya daga cikin wadanda suka amfana da aikin calculator ta gwamna domin kuwa suna samun albashin kafin 25 ga kowane wata.
Inda ya roki gwamnati data cike gibin maaikatan da ake dasu a maaikatu da hukumomin gwamnati tare da nada wakilan hukumar gudanarwar asusun adashen gata na fansho na jihad a kananan hukumomi.
Taken bikin na bana shine cutar corona da matsalar tattalin arziki da kalubalen samun aiki mai gwabi da bada kariya ga masu karamin karfi da kuma kyautata rayuwar alumma.
Comments
Post a Comment