ABIN MAMAKI:- Asalin Yadda Jahojin Nigeria suka samo sunansu da yadda asalin sunansu na farko yake..
Barka da shigowa wannan gidan na duniyar labari, gida ne da yake kawo muku labarai masu sanya nishadi, wasu labarai ne na zamanin baya wasu kuma na yanzu ne..
Yau cikin ikon Allah zamu kawo muku wani labari wanda aka jima ana tambayar mu su na yaya jahojin Nijeriya suka samo asalin sunansu.
Wasu suna son suji dalilin da yasa jihar da suke zaune ake kiranta da wannan sunan kamar jihar Jigawa ko Kano Kaduna da dai sauran jihohin Nijeriya.
Yau cikin shirin zamu fada muku duk yadda wadannan jihohin suka samu nasu sunansu.
Jihar Adamawa ta samo asalin sunanta ne daga wani mutum da ake kiransa da Modibbo Adama Hardo wanda shine ya kafa wannan bangaren.
Akwa Ibom sunan jihar ya fara ne daga sunan akwa iboe..
Jihar Anambra ta samo sunanta ne daga Oma Mbala
Jihar Bauchi itama ta samo sunanta ne daga wani da ake kiransa da suna Baushe wanda daga karshe aka mayar dashi Bauchi.
Borno suna ne wanda asali dama haka aka taso aka santa dashi babu labari akan yadda akai ta samu wannan sunan.
Cross river ya samo sunan ne daga kogin Oyono..
Enugu itama ta samo sunanta ne daga Enu Egwu.
Gombe itama ta samo sunanta daga fulani saboda dama asalin su fulani ne.
Jigawa ta samo sunanta ne daga tarin jigayin dake jihar.
Kaduna itama ta samo sunanta ne daga wata halitta da take ruwa wata Kada daga nan sai akai jam'i ake cewa gurin Kadduna saboda tarin kadojin dake wurin.
Kano asalin sunan wani makeri ne dake kere kere a gaya wanda da mutane suka fara taruwa sai aka sanyawa gurin ya zama Kano.
Katsina sunan matar wani mai gari ne da ake kira Janzama.
Kebbi itama ta samo asali ne daga Ka'aba dake saudi Arabia..
Kogi ta samo sunanta ne daga gurin taruwar ruwa mai gudana wato Kogi
Sokoto itama ta samo sunanta ne daga kalmar larabci Suk wato kasuwa tanan daga karshe sai aka juyata zuwa sokoto.
Yobe itama daga komadugu yobe ta samu sunanta daga karshe ta koma yobe
Taraba itama ta samo sunanta ne daga wani kogi tabara
Comments
Post a Comment