Abubuwan da kowacce mata ke son mijinta yake mata a koda yaushe
Koda yaushe akan yawan samun karuwar tambaya zuwa gare mu, na me mata ko kuma yan mata ke matukar son suna samu a gun samarinsu ko kuma mijinsu.
Wannan yasa muka karfafa bincike sannan muka samo muku wasu daga cikin abubuwan...
Wannan binciken bawai kai tsaye mukayi muku ba saida muka tattaro daga gurin mata masu yawa da kuma yan mata.
Wasu sun dauka kudi kawai zaka bewa mace shikenan zata soka ko kuma zata kaunace ka a'a kudi ba wata babbar hanya bace da za tasa yan mata ko matan aure suji dadin zama da mijinsu ko saurayinsu ba duk kuwa da cewa kudin ma suna taka rawa saidai ba irin wannan rawar suke takawa ba.
Koda baka bewa budurwa ko kwandala ba idan har tana samun wadannan abubuwan daga gareka shikenan ka mallake zuciyarta baza kuma taji koda wasa tana kaunar wani saurayin ko wani mijin ba.
Dan haka ga hanyoyin kamar haka:-
√ Bada lokaci:- wannan abinda na fada daga farkon ba karamin tasiri yake bayarwa ba tsakanin saurayi da kuma budurwa ko kuma miji da mata, ana yawan samun matsala ta rabuwa tsakanin masoya idan har saurayi ko miji baya bawa budurwarsa lokacinsa domin su tattauna ta wannan hanyar ne duk wasu matsaloli zasu gane su kuma su shawo kansu cikin sauki, kuma magana ta gaskiya mata suna matukar son wanda zai basu lokaci koda kallonsu ne ya tsaya yana yi za suji dadi kuma zasu kaunaci duk mai basu lokacin sa.
√ Kulawa :- Haba Malam mata suna matukar son ana kulawa dasu duk abinda suke so ana basu ba tare da fada ko kuma tambayar abinda za suyi ba.
√ Yabon kayan da suka sanya mata suna son idan sun sanya kaya kace musu sunyi kyau suna jin dadi sosai da sosai.
Kyauta :- Nasan kowa yasan yawan kyauta kan taimaka matuka wajen tafiyar da soyayya.
Iya kalamai:- Duk lokacin da ka iya kalamai to ka mallaki wani babban abu da zai baka damar tafiya da zuciyar wacce kake so dan haka ku koyi kalamai suna taimakawa sosai.
Comments
Post a Comment