An fara musayar maganganu tsakanin sojojin Nijeriya da Sheikh Gumi
Rundunar sojin Najeriya ta mayar da martani ga fitaccen malamin addinin musuluncin nan na kasar Sheikh Ahmad Gumi, da ya zarge ta da hada baki da yan bindigar da satar mutane da kuma kashe jama'a musamman a arewa maso yammacin kasar
Rundunar ta bayyana bacin ranta karara game da ikirarin malamin, wanda ta kira a matsayin wani abun haushi, da aka yi da manufar tozartartata da gan gan, da kuma nuna halin ko in kula ga jami'anta da suka rasa rayukansu a fagen daga.
Rundunar ta ce ''Yana da matukar muhimmanci mu nunawa jama'a cewa dakarun nan fa da ake zargi da hada baki da yan bindiga su din ne dai suka sadaukantar da tasu rayuwar suka ceto daliban makarantare sakandiren Yawuri''.
Rundunar ta kuma shawarci jama'a su kaucewa yin kalaman da za su sake ingiza 'yan bindiga su ci gaba da kai hare-hare a kan jama'a, tana cewa irin wadannan kalamai ba su dace da wadanda ake kallo a matsayin jagororin al'umma ba.
Comments
Post a Comment