Min menu

Pages

 



GOMA TA ARZIQI- part 1

SHIMFIDA

KADUNA, MALALI.

Tana zaune kan ‘tiles’ xin ‘bathroom’ ta haxa kai da gwiwa, idanunta na zubar da hawaye masu raxaxin da ta ke jin tamkar suna soya zuciyarta ne saboda zabar zafin da ta ke ji. A hankali ya turo qofar, ya tsaya yana kallonta kafin daga bisani ya kirayi sunanta murya qasa-qasa, “NUSAIBA”.

Ta xan xago kai ta kalle shi, tare da kai hannu ta share hawayen. 

Bai ce da ita komai ba ya qaraso daf da ita ya kamo hannayenta ya miqar da ita tsaye suna fuskantar juna. Hawayen ya qi tsayawa, sai sautin kukan da ke hanqoron qwace mata. Ta kifa kanta a qirjinsa yayin da ta sakar wa kukan linamin da ta yi qoqarin riqewa da farko. Ba shi da kuzarin rarrashinta duk da bai san damuwarta ba, rabuwa da ita ta more wa zubar hawayen zai fi maslaha a kan furta wata kalma da za ta iya havaka damuwarta, don haka kai tsaye ya nufi falo da ita. Suka zauna kan doguwar kujera yana shafa tsakiyar bayanta. Haka suka kasance tsayin mintoci kafin ta tsayar da kukan tana shessheka ta miqe tsaye.

“Ina za ki je?” Ya tambaya idanunsa kafe a kanta.

“Zan haxa maka ruwan wanka”.

Ya kaxa kai kawai ba tare da ya yi magana ba. Ta wuce ‘bathroom’, jim kaxan ta dawo ta sanar da shi. Ya miqe ya shiga, kafin ma ya gama wankan tuni ta shirya abinci kan ‘dinning table’. Suka zauna suna ci kamar yadda suka saba, ba ta cin abinci ita kaxai face ta samu tabbacin ba zai dawo gida a kan lokaci ba.

Bai tuhume ta komai ba har suka gama cin abincin, sai da ma ya dawo daga masallaci sallar la’asar sannan ya isko ta zaune gefen gado cikin ‘bedroom’ xinta. Ya zauna daf da ita yana akallonta.

“Yau kuma me ya haddasa min vacin ran farin cikina?”

Ta yi shiru kanta a qasa.

“Kina jina kuwa?”

Ta yi gyaran murya, tana saisaita nutsuwarta.

“Ba komai”. Ta ce a hankali.

Ya ce, “Ke ma kin san ba zan yarda da wannan ta zo mu ji-tan ba ko? Saboda haka ki sanar da ni abin da ya faru”.

Tsam ta taso daga mazauninta ta durqusa daf da qafafunsa.

“Ka yi haquri ka yafe ni Hubbi, na yi alqawarin zan yi maka biyayya, zan kiyaye duk wani abu da zai vata ranka. Amma na kasa jurewa, shekaru goma masu zafi da raxaxi ne a gare ni, waxanda suka jefa ni zullumi da tunanin anya na yi wa kaina adalci idan na ci gaba da goya wa zuciyata bayan bijirewa rubutacciyar qaddara ta?”

Ta qarashe furucin hawaye na zubowa a kumatunta, muryarta kuma ta raunana sosai.

“Saboda Allah ta ya zan iya gane wannan maganganun naki alhalin kin yi su a cure?” Ya faxa yana kallonta.

“Haka ne, abin nufi shi ne, rashin haihuwa na damuwa. Yana sa min fargabar cewar ba zan sake ganin qwaina a duniya ba”.

Nan da nan ya xaure fuska.

“Au wai dama wannan shi ne dalilin samar wa kanki sabuwar haramtacciyar xabi’ar zama a banxaki kina kuka? Wato kina so ki ce min kina kai qarar Ubangiji ga shaixanun da ke cikin banxakin ko za su samar miki da cikin haihuwa?”

Da sauri ta girgiza kai.

“Ba haka ba ne, ni ma ban san lokacin da hakan ta faru da ni ba”.

Ya ja gajeran tsaki.

“Muddin ba za ki cire wannan tunanin ba, to ba shakka za ki ci gaba da kasancewa cikin mafi qololuwar damuwar da ta fi haka. Kuma ni ban ga abin damuwa ba don mun yi shekaru goma ba ki haihu ba, in ba kina so ki nuna cewa kin gaji da zama da ni ba saboda kina zargin matsalar daga gare ni ta ke tunda ke kin tava haihuwa da wani namijin”.

Yadda ya yi furucin cikin vacin rai, sai ya raunana mata zuciya.

“Wallahi ba haka nake nufi ba. Haba Hubbi, yanzu kana tunanin duk GOMA TA ARZIQIN da ka yi min zan iya ture ta saboda zargin ba ka haihuwa?”

“To idan ba haka ba me ki ke nufi?”

Ta xan sunkuyar da kai, “Ina neman amincewarja ne ka sa baki su Inna su ba ni Ruqayyah ta dawo hannu…”

Mugun kallon da yake auna mata ne ya gurgunta furucin da ta yo dakon furtawa, tilas ta qarasa sunkuyar da kai yadda ta kauce wa ganin mugun kallon, amma zuciyarta na qara farshin bugawa tamkar qirjinta zai fashe.

“Uhum? Ci gaba mana! Ko ba kina son ki nuna min zahirin qiyayyar da ki ke yi min a dalilin xan iskan uban ‘yarki ba? To daxin abin wanda ya mutu ba zai tava dawowa ba, wataqila da ni ma na bi sahunsa na kashe aurena don ki cimma burin rayuwa da shi”.

Ba qaramin duka kalamansa suka yi mata ba, yadda ta kasa shanye xacin da suka samar mata a zuciya, ba ta ma san sanda ta ce, “Wace irin magana ce ka ke furtawa haka Hubbi? Ta ya za ka aibata mutumin…”

Wata firgitacciyar tsawa ya daka mata, “Ke da Allah rufe min baki! Har kin isa ki taka min birki a kan fitinannen mutumin da ya murqushe duk wani tanadi da na yi wa rayuwata na mallakar zuciyar matata? Ko kina tunanin akwai wani furuci da zan yi ga mutumin da ya wulaqanta rayuwarsa? Ba da ni ba wallahi, kuma zan ci gaba da aibata shi har qarshen rayuwata”.

Ranta ya vaci sosai, ta miqe tsaye.

“Na gode da cin mutuncin da ka yi…”

Ta kasa qarasa maganar sakamakon kukan da ya qwace mata, ta ruga da gudu zuwa falo tana jin zafi da raxaxin kalaman mijin nata ga mutumin da ya zamo uban ‘yarta qwaya xaya tilo. Kan doguwar kujera ta faxa tana kuka mai dalili, wai ISMA’EEL ne xan iska, kuma fitinanne? Waxannan kalamai sun fi komai vata mata rai, amma ba ta da haufi ko inkari, duk abin da ya samu shamuwa watan bakwai ne ya ja mata. Sai dai hakan ba yana nufin za ta zuba idanu a ci gaba da aibata gawar Isma’eel ba. Abin da ya aikata tsakaninsa ne da Ubangijinsa, tunda matsayinsa na uban ‘yarta ba zai tava kankarewa ba, to ba za ta sarayar da wannan qimar ba, dole za ta yi fito-na-fito da duk wanda zai aika wa gawarsa mugun saqo na hana masa kwanciyar kabari lafiya.

Tana kwance tana kukan, ya fito daga xakinta. Kallo xaya ya yi mata ya ja tsaki, har ya kai qofar xakinsa zai shiga ya juyo yana kallonta.

“Kuma ki sani zan juri komai a gidan nan, ban da sha’anin da ya shafi annamimin uban ‘yarki ba, muddin ba ki kiyaye hakan ba, to kuwa ki xaura xamarar xaukar kowace irin rayuwa da hakan zai haifar”.

Ya wuce xakinsa ya barta cikin jin kamar ta tashi ta mayar masa da martani. Sai dai ta kasa hakan.

Rana ta farko komai ya kwave musu a tarihin rayuwar aurensu na shekaru goma. Ta gumtsi fushi mai tarin yawa ta qawata fuskarta da shi, ta qi ba shi damar da za ta haxiye shi ballantana ta tuna matsayinsa na mijinta da aljannarta ta ke qarqashin qafarsa. Yayin da shi ma ya fi ta hawa kamar kwavavviyar fulawar da za a yi cin-cin da ita bayan ya gama zamansa a xaki ya fito misalin shida saura ya bar mata gidan. Bai dawo ba sai goma da rabi na dare, bayan ya ciko cikinsa a restaurant, saboda vacin ran da ta saka masa ba zai iya barinsa ya ci abincinta ba.

Tana jin shigowarsa ko motsi ba ta yi ba, ballantana ta je gare shi. Ko jin akwai wani haqqinsa da ke kanta na kula da abincinsa, ko gurin kwanciyarsa da ya zama wajibcin gudanarwa a gare ta kafin wannan ranar, hasalima ko kaxan ba ta sha’awar ganin fuskarsa, saboda laifin da 

Comments