Min menu

Pages

Gwamnatin Tarayya ta kashe Dala Biliyan 5 domin fitar da Yan Najeriya Talauci a cikin Shekaru 5

 Gwamnatin Tarayya ta kashe Dala Biliyan 5 domin fitar da Yan Najeriya Talauci a cikin Shekaru 5



Ministar Jinkai da Walwala Hajiya Sadiya Farouq tace Gwamnatin Tarayya ta kashe Dala Biliyan 5 tun daga Shekarar 2016 domin yakar Talauci a Najeriya.


Ministar tace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari,  tun daga Shekarar 2016 zuwa yanzu yake cika alkawararin daya dauka na fitar da 'Yan Najeriya Miliyan 100 daga kangin Talauci, ta hanyar bayar da Dala Biliyan 1 a shirin tallafi kudi kyauta domin rage radadin Talauci.


Ta kuma bayyana gaskiyar  Shugaba Buhari na magance Talauci, Wanda a cewar ta, Kimanin Yan Najeriya Miliyan 7.5 an fitar dasu daga Kangin Talauci.


Shugaban Shirin Bayar da Tallafin na Kasa Wanda ya Wakilci Ministar, shi ya bayyana haka a ranar Asabar a Yola, a lokacin da aka rarraba Wayoyin hannu ga Mutane 248 domin su kula da shirin a Adamawa.


Tace" Ina farin cikin Sanar daku cewa duk Shekara tun daga 2016, duk lokacin da aka kaddamar da fara Shirin, Shugaba Buhari yana amincewa da fitar da Naira Biliyan 1 domin sanyata a Shirin, Wanda yanzu ya kama Dala Biliyan 5"

Comments