IDAN NAJERIYA BATA HALASTA MAƊIGO DA LUWAƊI BA TO BA ZAMU SIYAR MATA DA MAKAMAI BA—AMURKA
Kasashen Amurka da China na gasar samun karfin Iko a Nahiyar Africa. Sai dai suna da banbancin ra’ayi kan yanda suke wannan gasar. A ɓangare ɗaya, kasar China ta fi baiwa ɓangaren Kasuwanci da gina guraren ci gaban al’umma dan cimma Burinta.
Sai dai kuma tana amfani da wannan dama wajan yiwa ƙasashen Africa leken Asiri da tatsar bayanan Sirrinsu. Tana amfani da waɗannan bayanai ne dan ta san hanyar da zata samarwa Africa kayan amfani da suka yi daidai da mutanen Nahiyar dan shiga gaban ƙasar Amurka a gasar da suke, sannan kuma da wasu boyayyun manufofinta da ba’a kai ga sani ba.
A shekarar 2017 wani kwararre dake aiki da Hukumar Hadin kan Nahiyar Africa ta Africa Union ya gano wani lasifikoki da mahnajoji da ak makala a jikin ginin Hedikwatar kungiyar dake Ethiopia. Suna aikawa kasar China bayanai ne kan yanda Nahiyar Africa ke gudanar da al’amuranta.
Kwararru sun taru aka cire wadannan lasifikoki aka mayesu da wasu. Kasar China ta yi Amfani da wannan dama tana tatsar bayanai daga Africa tsawon shekaru. Wani abin mamamki, ko kuma a kirashi da rashin kunya, shine, da aka zo canja wadannan lasifikoki, kasar China ta yiwa Africa tayin cewa, zata canja mata su amma aka ki amincewa.
Saidai kuma Chinar ce dai ta ginawa Africa wancan gini kyauta da darajarsa ta kai Dalar Amurka Miliyan 200. Saidai bayan kammala ginin, ta saka na’urori da take tatsar bayanai daga Africa.
China ta ginawa kasashen Africa da dama Titunan Jirgin kasa da Filayen jiragen sama da Titunan motoci da gada da sauransu.
A bangaren guda kuma, Zuwan Kasashen Amurka da Faransa Nahiyar Africa, musamman Africa ta yamma, kusan za’a ce bai amfanar da yankin da komai ba, kamar yanda Defence Nigeria ruwaito.
Kasar China na kuma Amfani da Kasashen Africa wajan samun ma’aikatan da zata biya albashi ba ne yawa ba, saboda yanayin tattalin arzikin Nahiyar, saidai za’a ce hanyar kasar China ta fi ta Amurka da kasashen T
Comments
Post a Comment