Jerin kasashen Afrika 13 suka canja suna bayan sun samu yancin kai
Assalamu alaikum ma'abota bibiyarmu a wannan gidan na duniyar labari, hakika muna jin dadin yadda kuke biye damu wannan ba karamin farin ciki yake samu ba.
Wannan gidan guri ne da yake kawo labarai da tarihi iri iri, dan haka yau cikin shirin namu muna tafe muku ne da jerin wasu kasashe a cikin Afrika wanda suka canja sunansu lokacin da suka samu yancin kai daga gurin turawan da suka mulke su a baya.
Ghana kasar gana a farko bawai wannan sunan shine sunanta ba ta asalin sunan kasar Ghana shine Gold Coast amma sun canja sunan ne zuwa Ghana a shekarar 1957.
Mali kasar mali ma bawai haka sunanta na ainashi ba sunanta french sudan to lokacin da ta samu yancin kai ne ta koma Mali a shekarar 1960.
Botswana asalin sunan wannan kasar kafin su samu yancin kai shine bechuanaland to bayan ta samu yancin kai ne ta koma Botswana a shekarar 1966.
Congo Democrat Republic itama da ba wannan sunan bane asalin sunan ta ba sunanta Belgian Congo data samu yancin kai ne aka canja sunan kasar.
Mozambique da itama wannan kasar ba haka ake kiranta ba kafin ta samu yancin kai ana kiranta ne da Portuguese east Africa data samu yancin kai ne ta koma haka
Angola da sunan da ake ce mata shine Portuguese west Africa kafin ta samu yancin kai.
Burkina Faso itama da wannan sunan bane asalin sunanta saida ta samu yancin kai ne ta koma haka daga wannan sunan haute Voltaire.
Comments
Post a Comment