Limamin Ka’aba mai tsarki ya ziyarci Gwamna Zulum, ga abinda yace masa
Lokacinda suka hadu yace muna kallon dumbin nasarorin da ka samu a jihar Borno.
Farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari, wani malamin Saudiyya kuma daya daga cikin Limaman da ke jagorantar sallar jam’i a Masallacin Ka’ba (masallacin Al-Haram) da ke Makkah, ya kai ziyara ga Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, kamar yadda majiyar Madubi-H ta ruwaito.
Ziyarar da aka yi da yammacin Laraba a gidan Gwamnati, Maiduguri.
Imam Bukhari, wanda shi ne shugaban tsangayar karatun Larabci ga wadanda ba ‘yan asali ba a Jami’ar Ummul Qura da ke Makkah, ya je Maiduguri ne bisa gayyatar Dr. Mohammed Kyari Dikwa, Shugaban Gidauniyar Al-ansar da ke gina jami’a mai zaman kanta ta farko a Borno. a wani wuri a cikin Maiduguri.
Comments
Post a Comment