Min menu

Pages

ME YA SA BA ZAMU HADU DA MASIFA DA BALA'I BA A NIGERIA

 ME YA SA BA ZAMU HADU DA MASIFA DA BALA'I BA A NIGERIA



Anya kuwa zamu wanye lafiya alhali mun siffantu da wadannan miyagun dabi'u? 

👇

(1) Principal (Shugaban makarabtar sakandare)  yaci kudin feeding na yara, yaci kudin NECO da WAEC na yara, yaci kudin registration na makaranta


(2) Jami'an tsaro da bindigarsu su karbi Naira ashirin a hannun direban motar fasinja, su ki duba mota akan Naira 20, su bar mai laifi ya wuce


(3) Dan fashi da makami a kama shi sau dari idan yana da kudi Lauyoyi su tsaya masa a sake shi sau dari 


(4) Mai garkuwa da mutane idan an kamashi Lauyoyi su kubutar dashi idan yana da makudan kudi


(5) Babban Malamin jami'a Professor  shi daya tak yake aikin mutum biyar yana karban kudi double, sannan da shi ake zagin Gwamnati wai bata daukar ma'aikata

Dalibi ya zo karatun Masters ko PhD, Professor ya rike shi shekaru goma bai gama ba, don kar ya gama ya kamo matsayinsa saboda hassada da mugunta


(6) An zo bada tallafin noma, mutumin da idan kace masa menene "Kadada" daya ko "Kunya" bai san me ake nufi ba, amma kuma yaje ya karbi injin ban ruwa ya sayar naira dubu uku.

'Dan kwangilar da aka baiwa sayan wannan kayan shi zai zaga ya sake saya ya kai wani garin kuma ya sayar da tsada


(7) Mai sana'ar awu a kasuwa ya tauye mudu ga wanda zai saya,  idan shi zai saya ya cika mudu saboda ha'inci


(8) Talaka ya buge geronsa da ya noma, idan ya tashi kaiwa kasuwa ya sayar sai ya hada da butacin geron a buhu ya kai kasuwa domin yayi masa auki saboda ha'inci


(9) Idan makiyayi ya tashi sayar da saniyarsa a kasuwa, sai ya nemo magani mai kara kuzari ko kumburawa ya bawa saniyar ko da bata da lafiya, domin a ganta da lafiya a saya da tsada yaci riba saboda ha'inci


(10) Mai sana'ar sayar da kaji, idan ya tashi sayar da kajinsa ana saura kwana uku sai ya musu allurar da zai kumburasu su kara nauyi, yaje ya sayar a kasuwa,  mutane su sayi cuta ko ciwo ko gembo suci,  wai sunci nama, ba su sani ba cuta sukaci,  saboda mai kaji yayi ha'inci don yaci riba


(11) Idan ka bawa 'yan kwadago noma a gonar ka, sai su sare wata ciyawar, wata ciyawar kuma su binne da kasa, a karbi kudinka a tafi an gama aiki, bayan kwana biyu ka ga gona tayi ciyawa


(12) Ka tura danka makaranta, sai yayi maka karyar cewa ance su kawo dubu goma, idan ka tura masa kudin sai yaje ya sayawa budurwarsa a makaranta taliyar indomi da kwai, mahaifiyarsa  kuwa ko a watan Azumi bai iya saya mata kwai ba, ka bawa matarka kudin cefane ta rage


(13) Babban Ma'aikacin gwamnati ya sace dukiyar al'ummah, yaci kudin hutu na ma'aikata,  yaci kudin fansho da giratuti na wadanda sukayi ritaya


(14) 'Yan siyasa su danne hakkin talakawan da suka sadaukar da rayukansu suka zabe su, da zaran sunci zabe sai su canza layukan waya,  basa sake waiwaitar mutanensu sai bayan shekara hudu


(15) Sarakunan gargajiya su karbi kudi a hannun 'yan siyasa su sayar da ruhi da rayuwar talakawansu


(16) Miyagun Malamai maciya amana su karbi kudin 'yan siyasa, shikenan an rufe bakinsu kirif, suna ji suna gani ana kashe al'umma, ana yakar addini amma ba zasuyi magana ba,  saboda sunci kudi


(17) 'Yan kasuwa suna sayan abinci su boye sai yayi tsada su sayar,  suna sayan matattun abubuwa su sake fanti su sayar a matsayin sabo, saboda cuta da ha'inci


(18) Mai aikin gyaran wuta ka bashi kudin waya mai kyau, amma sai ya rage ya sayo maka marar kyau ya hada, bayan kwana biyu gobara ta kama gidanka


(19) Malaman addinin Musulunci da Pastor Malamin addinin Nasara, a dauki dukiyar gwamnati a kaisu Israila da Makkah, da dukiyar al'umma wanda ya kamata a gyara asibiti da makarantun gwamnati dashi


(20) A hada baki da mai unguwa a sayar da kayan marayu


(21) Ana cin hakkin makwabtaka, makwabci ya nemi matar makwabcinsa,  makwabci ya kwana da yunwa alhali makwabcinsa yana da abincin shekara guda a ajiye, anci amana kuma an ki zumunta don Allah, idan ka ga ana zumunci da kai to kana da dukiya


(22) Wadda kuke addini daya ko kabila ko yanki daya idan yayi laifi sai kace sharri aka  masa saboda ba'a son gaskiya


(23) 'Yan Jarida sun zamo makaryata da masharranta saboda neman kudi ta kowani hali,  ba su damu da kare martaban kasar su da addininsu da yankin su ba


(24) Ka wuni a Majalisa kana kalle-kallen matan mutanr da cin naman mutane da zagin mutane


(25) Ana baka karamar dama da amana ka ci, kayi babakere akan dukiyar da ba taka ba kazo kana alfahari


(26) Ka fadi magana ka zabga karya ba tare da shaida ba


(27) Alkalai sun zamto 'yan amshin shata


(28) Ka haifi yara ka kasa kula dasu su zama 'yan iska su addabi kowa su hana kowa zaman lafiya


(29) Hukumar zabe ta daure gindin magudi


(30) Masu Karfi sun dena tausayin marassa karfi


(31) Tela babu cika alkawari


(32) Lebura ha'inci.


(33) Masu sai da kaya cuta, zamba, algus da almundahana


(34) Maza yaudara


(35) Mata kwadayi


(36) Zina, Luwadi, Madigo, Zina da dabbobi, Shan jini, Kisan gilla ya zama ruwan dare a tsakanin al'ummah


(37) Rowa, Annamimanci, Hassada, Kyashi da Mugunta ya zama cutuka mafi yaduwa a tsakanin al'ummah


(38) Ka samu daukaka, na kusa da kai suna maka hassada


(39) Masu gidajen mai suna so ayi karancin mai domin suci babbar riba


(40) Nepa sun saka maka meter kayi byepass


(41) Ka saci ruwan water board ka fasa pipe


(42) Kaci iyakar gonar makwabcin ka


(43) Ana layi kayi cuwa-cuwa kayi shan kai


(44) Ka barnatar da dukiyar gwamnati


(45) Ka ki biyan haraji


(46) Ka ki bin doka da order


(47) Ka cutar da makwabtanka ta hanyar zubar da shara da kazanta


(48) An hada baki da 'yan shugabannin kwadago an cutar da ma'aikata


(49)=An dauke ka aiki kayi wata da watanni bakaje aiki ba, amma kana karban albashi duk wata


(50) Lauya yayi shaidar zur


(51) Likita yayi wasa da lafiyar mutane


(52) Bankuna sun ci haram sun tu'ammali da kudin ruwa


(53) Ka bar dabbobin ka suna ta'adi wa mutane


Tambaya a nan:

Shin idan bamu gyara halayen mu ba, muna da hurumin zagin gwamnati?

Mune fa gwamnatin, daga cikin mu Allah Ya zakulo mana Shugabannin, ba daga sama suka fado ba, iyayen mu ne, yayun mu ne, kannen mu ne. Muryan Arewa Reporters 


Ko a Kasar da basu taba sanin akwai Allah ba idan suka siffantu da wadannan miyagun dabi'u dole su fuskanci masifa da tashin hankali, balle Kasar da suke Musulunci


Allah Ka bamu ikon gyara halayen mu Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Comments