Mutum Ukun nan sune ke juya kannywood ga sunansu kamar haka
A yanzu dai idan aka duba yadda masana’antar finafinai ta Kannywood ta ke tafiya kusan za a iya cewa tana hannun wasu mutane duga uku, wadanda a yanzu dai su ne su ke juya ta, kuma a yadda suka ga dama, kuma a haka a ke sha, don haka kusan duk wanda ka gani a masana’antar a yanzu to dole ne za ka same shi yana tare da daya daga cikin mutane ukun nan
Ko mutane nawa za'a kashe saidai a kashe amma sai mun kafa kasar Biafra inji Nnamdi Kanu
Farko dai akwai Furodusa Bashir Abubakar Mai shadda, wanda a yanzu babu wani Furodusa da ya ke motsi a cikin masana’antar sai shi kadai, wannan ta sa duk in da ka ji ana yin aikin wani fim in dai na Kannywood ne, to yana da wahala a ce, ba shi ba ne a matsayin Furodusa, don haka ya ke da karfin fada a ji.
Na biyun su kuma shi ne fitaccen Mawaki Dauda Kahutu Rarara, duk da shi ba ya fito ya bayyana kan sa a matsayin dan fim ba ne, amma saboda tasirin da waka take da shi ya sa ya jawo duk wani jarumi ya saka a aljihun sa, domin idan zai shirya waka ya kan kwashe dukkan jarumai maza da mata ya tafi da su duk in da ya ke so. Abin da ya sa kuma ya ke da tasiri a wajen ‘yan fim shi ne yadda ya ke raba Motoci da kudade kamar yadda a ke raba gyada. Wannan ta sa ya ke da karfin fada aji
Na ukun su kuma shi ne Abdul Amat wanda a ke yi wa lakabi da mai kwashewa. Furodusa ne, wanda da ya samu dama sosai a wajen’ yan siyasa, domin haka ya ke da karfin fada a ji. Ba komai ya jawo masa wannan tasirin ba, sai don yadda ya ke raba kayan abinci da kudade ga ‘yan masana’antar, ko da ya ke shi ma a’yan kwanakinnan ya fara rabon Motoci. Don haka a yanzu babu wasu da suke rike da masana’antar sai wadannan mutane, don har ana ganin ba don su ba, da tuni jarumai da dama sun fara yawon bara.
Comments
Post a Comment