Min menu

Pages

Twitter da sauran manyan kafafen sadarwa na zamani sun nunawa duniya karara a tsagin da su ke

Twitter da sauran manyan kafafen sadarwa na zamani sun nunawa duniya karara a tsagin da su ke



Daga Shafi'u Dauda Giwa


Duk da wasu suna kafa hujjar kafin su goge kalaman shugaba Buhari, kalaman Donald Trump su ka fara gogewa, wannan ba zai sa mu yarda cewar da a ce wani Dan kudu ya ke mulki Yan arewa su ke yi masa tawaye za su goge kalamansa ba koda kuwa me ya furta a kanmu


Ba iya Nigeria wannan banbancin ya tsaya ba, wannan ka'ida ce ta zamantakewar duniya tsakanin kasashen da ke fada a ji, da kuma kananan kasashen da a ke yiwa kallon hadarin kaji


Shiyasa har yau babu abin da ya fi komai damuna a duniya irin rarrabuwar kan kasashenmu na musulmi, wanda hakan ya taimaka wajen harhadawa sauran kasashen yahudawa da kawayensu karfin murkushe duk wanda ba su so da makamin magana da makamin kisa


Tsanar a bayyane ta ke, duk kasar da kiristoci su ke komai kankantarsu su ne yayan mowa a idonsu, sannan duk in da musulmai su ke sai an bi su da bita da kullu an musguna ma su


A rikicin shugaba Buhari da Tweeter mu na tare da shugaba Buhari dari bisa dari ya yi daidai da ya ja masu layi


Amma wannan ba zai hana idan a ka dawo cikin gida shima ya yi ba daidai ba mu ja masa layi


Mu yan tsakiya ne, duk in da gaskiya ta ke ko a ina ne mu na bayanta

Comments