An jefa ni cikin yanayin dimuwa da damuwa yanzu haka- Nnamdi Kanu
Shugaban haramcaciyar kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi kanu ya koka akan abinda ya kira cin zarafin da ake masa a inda ake tsare shi a Hukumar Tsaron farin kaya ta DSS tun bayan mayar da shi Najeriya domin fuskantar tuhumar da ake masa na cin amanar kasa.
Kanu ya gabatar da bukatar sa ga Babbar Kotun Abuja inda yake bukatar ta bada umurnin fidda shi daga hannun jami’an tsaron DSS domin mayar da shi gidan yarin Kuje.
Tun bayan tasa keyar sa da jami’an tsaro suka yi zuwa Najeriya, mai shari’a Binta Nyako da ta bada belin sa a shekarar 2017 kafin ya gudu ta baiwa Hukumar DSS umurnin aje shi har zuwa ranar 26 ga wannan watan da zata ci gaba da sauraron tuhumar da ake masa.
Bukatar da lauyan sa Ifeanyi Ejiofor ya gabatar wa kotu ta bayyana cewar wanda yake karewar na cikin yanayin demuwa da rudani a inda ake tsare da shi, saboda haka yana bukatar mai shari’a da ta masa adalci wajen mayar da shi gidan yarin Kuje
Lauyan yace Kanu baya samun kula da lafiyar sa kamar yadda ta dace da shi a hannun jami’an tsaron farin kayan saboda yanayin da yake ciki, saboda haka yana bukatar kwararrun jami’an kiwon lafiya su kula da shi kamar yadda Babban jami’in kula da lafiyar asibitin Nairobi ya bayyana a rahotan da ya rubuta kafin kama shi.
Ejiofor yace rashin baiwa Kanu kula da lafiyar da ta dace na iya haifar da mutuwar sa a inda ake tsare da shi, kafin gudanar masa da shari’a.
Lauyan yace tun da aka shigar da shi Najeriya ranar 27 ga watan Yuni, Hukumar DSS ke tsare da shi a daki shi kadai inda baya ganin kowa daga cikin iyalan sa da suka hada da matar sa da ‘yan uwan sa da kuma ‘yayan sa, sai dai kawai lauyan sa bayan ya samu umurnin Darakta Janar na Hukumar DSS.
Ejiofor yace Kanu na ci gaba da fuskantar dimuwa da azabtarwa a inda ake tsare da shi yanzu haka.
Comments
Post a Comment