Min menu

Pages

Ɗan sanda ya kashe mutumin da kotu ta wanke kan zargin ɓatanci ga Annabi

 Ɗan sanda ya kashe mutumin da kotu ta wanke kan zargin ɓatanci ga Annabi



Wani ɗan sanda a Pakistan ya kashe wani mutum da adda kan zargin yin ɓatanci ga addinin Islama, shekaru bayan kotu ta wanke shi, kamar yadda ƴan sandan ƙasar suka bayyana a ranar Asabar.


Waqas y fuskanci shari’a a 2016 kan wani saƙon da ya wallafa a Facebook, amma daga baya kotu ta wanke shi.


Ɗan sandan mai suna Abdul Qadir, ya fusata da hukuncin kuma a ranar Juma’a ya kai masa hari da daddare a garin Rahim Yar Khan da ke yankin Punjab.


“Ya daɗe yana son kashe shi tun 2016 kan zargin da ake masa na yin ɓatanci ga Annabi Muhammad,” kamar yadda ƴan sanda suka shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP.


Kakakin ƴan sandan Pakistan Ahmed Nawaz ya tabbatar da faruwar al’amarin inda ya ƙara da cewa an ɗan sandan ya kuma yi wa ɗan uwan mamacin rauni.


“Jami’in ɗan sandan da kansa ya miƙa kansa ga ƴan sanda bayan aikata kisan,” in ji shi.


Yin ɓatanci ga addini babban al’amari ne a Pakistan, inda za a iya zartar wa mutum hukuncin kisa ga duk wanda ya yi ɓatanci ga addinin Islama

Comments