Hassada ce kawai ta sa ake sukar shirin wasan kwaikwayon ‘A Duniya’ – Tijjani Asase
Tun bayan shefe kusan watanni biyu da tafiya hutun haska Fim ɗin nan mai dogon Zango na ‘A Duniya’ wanda ya janyo al’umma ke raɗe raɗin cewa hukumomi tsaro da sauransu sun dakatar da nuna fim ɗin sakamakon ana zargin Fim ɗin da ƙara tallata harkokin daba da kwacen wayoyi a jihar Kano.
To sai ga shi marubuci, Jarumi kuma ma shiryin shirin na ‘A Duniya’ Tijjani Abdullahi (Asase) ya ƙaryata batun inda ya danganta haka a matsayin hassada da rashin son ci-gaban su da wa su suke mu su kamar yadda ya bayyana wa Labarai24, ya yin wata tattunawa da ya yi da Labarai24 kan batun yadda wasu daga cikin ɗai ɗaikun Al’umma ke dangana Fim ɗin da ɗaukar wata hanya da ake ganin zata jawo cigaban ayyukan daba a sassan jihar Kano.
Wanda ada kan a dawo da cigaba da haska wannan fim na ‘A Duniya’ ya ɗauki tsawon lokakaci wanda harta kai ga sa ran hukumomin tsaro ne suka shiga tsakani domin hana wannan Fim.
Ta cikin tattaunawar Asase ya ce “kamar yadda al’adar finafinai masu dogon zango su ke a ko ina akan ɗauki tsawon lokaci idan angama da ɗaukar farko kan a shiga ta biyu wato ‘season’ ke nan to wannan ma hakan ne ya faru, duk wani aiki mai wahala yakan ɗauki lokaci kamar yadda mu ma mu ka yi” .
Da Labarai24 ta tamabayi Asase kan raɗe raɗin da mutane ke yi na dakatar da nuna fim ɗin sakamakon ana zargin su da tallata harkokin daba da ƙwacen waya, sai jarumin ya ce “Wai makaho ne ya ce a yi wasan jifa ka san ai akwai abinda ya taka, indai ba akwai abinda ya taka ba ya za a yi ya yi, don haka duk mutumin da kaji yana cewa ka-za-ka-za idan ba ka son abu ba ka son sa idan kana son abu kana sonsa, saboda abune a buɗe wanda daman ba ya son sa dole ne ya kawo kushewa a kai, finafinai nawa aka yin akasin fim ga sunana wanda kuma tuntuni ake yin su kamar irin su Basaja, ga kuma finafinan Indiya nan wanda ake tace su ake yi da Hausa duk ga sunan, sannan idan finafinan ‘yan daba ake magana me ma aka yi a fim ɗin A Duniya?
Duk cikin Fim ɗin babu inda aka nuna an sari wani babu inda aka nu na an ɗauki wuƙa aka bugawa mutum to menene abin da ake a ciki? Kawai dai abu ne da Allah ya sa masa albarka kuma surutun mutane ba zai ƙare ba.
“Mu ƴan Kano ne ƴan birni muna da iyaye muna da surukai muna da ƴan uwa, in ka yi abinda ya dace ka sa ni in ba ka yi ba ma ka sa ni duk kuma wani abu da za ka samu a gidan duniya ne, sannan duk wani abu da za ka yi kayi ƙoƙari ka gyara lahirar ka”.
Ya kuma ƙara da cewa “Na ƙirƙiri Fim ɗi na ne ba akan Daba ba sai akan son zuciya irin na ɗan-adam, a nunawa mutane cewa da kowanne zai cire son zuciyar da yake ransa da Duniya ta zauna lafiya, da kai kanka zaka cire na ka son zuciyar ni ma na cire nawa wancan ya cire na sa to da mun zauna lafiya”
”A ko da yaushe mutane su dinga fatan alkhairi akan mutane mana, na farko dai yanzu abinda ake so a nunawa mutane shi ne mutum ya dogara da kansa ba wai ya yi tunanin sai yayi aikin gwamnati ba, idan ka duba zaka ga ɗumbin mutanen da su ke cin abinci ta cikin wannan fim na wa kuwa? Ya kama mutane su dinga bawa mutun kwarin gwiwa idan ya samawa kansa aikin yi ba wai a dinga daƙile shi ba, don haka yanzu mu yi ƙoƙari mu koyawa samarinmu yadda za su samu abinda da za su ci su sha ba wai yadda za su zama maƙiyanmu ba a rayuwa”.
Shirin ‘A Duniya’ dai shiri ne da ake nuna wa a tashar YouTube mai suna Zinariya wadda take mallaki ga Jarumi Tijjani Asase, shirin da ya ke nuna wasu daga cikin halayyar son zuciya da matasa suke nunawa ta hanyar kashe zuciyarsu tare da yin sa-ce-sa-ce wanda har ta kai su ga dana sanin rayuwa.
‘A Duniya’ wanda aka ɗauki tsawon shekara 1 da fara yin sa za a cigaba da haska kashi na huɗu bayan da aka gama gashi na ɗaya da na biyu harma da na Uku.
Comments
Post a Comment