Hukumar NCDC Ta Gargadi Musulmai Game Da Yawon Babbar Sallah, Don Kaucewa Kamuwa Da Cutar Corona A Karo Na Biyu
Yayin da musulmai masu ke shirin bikin sallah babba a mako mai zuwa, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta yi gargadi game da tafiye-tafiye a lokacin bukukuwan sallah.
Shugaban NCDC na Sashin Sadarwa, Dakta Yahya Disu, shi ne ya bayar da wannan gargadin a ranar Laraba yayin shirin karin kumallo na gidan Talabijin din Channels.
Disu ya ce karo na biyu na annobar Corona ta fara ne a Nijeriya saboda mutane sun yi tafiya don Kirsimeti a Disambar da ta gabata.
Don haka, ya bukaci 'yan Nijeriya da su guji tafiye-tafiye marasa mahimmanci a lokacin bukukuwan sallah na mako mai zuwa.
Ya bukaci shugabannin addinai da su wayar da kan mabiyansu a kan wajabcin kiyaye ka’idojin Korona domin kiyaye karuwar yaduwar cututtuka.
Disu ya ce: "Mafi mahimmanci, sallah tana zuwa, lokacine da mutane ke tafiye-tafiye kuma hakan na kara hadari ga kauyuka, a sassa daban-daban na kasar.
"Don haka, muna bukatar fadakar da mutane: ba sa bukatar tafiye-tafiye idan ba dole ba ne, za ku iya yin biki a inda kuke.
A lokacin sallah, muna zuwa masallaci adadi mai yawa kuma wannan shine lokacin da ya kamata mu kiyaye.
Comments
Post a Comment