Jerin jahoji da sukafi yawan masu cutar kanjamau (HIV) a kasar Nigeria
Cuta mai karya garkuwar jiki ita ake kira kanjamau, wacce da zarar ta kama mutum to magana ta gaskiya da wuya ya warke saboda har yanzu an gagara samo takamaiman maganinta wanda idan mutum ya sha zai warke sumul duk da cewa akwai masu magungunan da suke cewa suna bada maganinta amma dai har yanzu duniya bata yadda akwai maganin cutar sadidan ba wanda ake warkewa idan an sha.
Ita wannan cutar idan mutum ya kamu da ita to fa shikenan kusan duk wani da yayi tarayya dashi ta hanyar saduwa shikenan shima ya kamu da irin wannan cutar
Hanyar kamuwa da wannan cutar
Kusan hanyoyin kamuwa da wannan cutar ba daya bane sunada yawa amma akasari anfi kamuwa da ita ta hanyar jima'i domin kaso 99.8% na masu cutar ta haka suka kamu.
Jerin jahojin da sukafi yawan masu wannan cutar
Akwa Ibom 5.6%
Benue 4.9%
Rivers 3.8%
Taraba 2.7%
Anambra 2.4%
Enugu 2.1%
Abia 2.1%
Delta 1.9%
Nasarawa 1.9%
Edo 1.8%
Bayelsa 1.8%
Cross River 1.7%
Imo 1.6%
Plateau 1.5%
FCT 1.5%
Lagos 1.3%
Borno 1.3%
Adamawa 1.3%
Ogun 1.2%
Gombe 1.2%
Kaduna 1.0%
Kogi 1.0%
Kwara 1.0%
Ondo 0.9%
Osun 0.9%
Oyo 0.9%
Ebonyi 0.8%
Niger 0.7%
Ekiti 0.7%
Kebbi 0.6%
Kano 0.5%
Zamfara 0.5%
Yobe 0.4%
Bauchi 0.4%
Sokoto 0.4%
Jigawa 0.3%
Katsina 0.3%
Comments
Post a Comment