SHIKENAN SHIMA KWAMANDAN IPOB YA SHIGA HANNU
Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari ya kama babban kwamandan Eastern Security Network (ESN) reshen IPOB karkashin jagorancin tsageri Nnamdi Kanu mai suna Emeoyiri Uzorma Benjamin wanda aka fi sani da Onye Army
Onye Army yana da hannu wajen salwantar da rayukan jami'an tsaro a jihar Imo, da kashe fararen hula, da kona ofishin jami'an tsaro da fasa gidan yari, sannan shine ya jagoranci hari a gidan Gwamnan jihar Imo domin mayar da martani sakamakon kashe Ikonso kwamandan IPOB da dakarun Abba Kyari sukayi kwanaki
Bayan kwamandan ESN Onye Army ya shigo hannun Sarkin Yaki DCP Abba Kyari, an bar 'yan jarida sunyi hira dashi, ya bada cikakken bayani akan ayyukansu na ta'addanci da irin umarnin da Nnamdi Kanu yake basu
Yace lokacin da aka kashe Ikonso, shugabansu Nnamdi Kanu ya umarcesu da su bunne gawar Ikonso da kawunan mutane dubu biyu, amma kawunan mutane 30 kadai suka kashe suka cire kawunansu, sannan sunyi amfani da kawunan 'yan mata guda 10 wajen hada tsafi domin samun kariya daga harsashin bindiga na 'yan sanda
Yayi dogon bayani akan dalilin shigarsa kungiyar ESN da manufar kafa kungiyar, yace Nnamdi Kanu ne ya kafa a 2020, ya umarcesu da su ruguza dukkan sansanin jami'an tsaro da ofisoshin su a jihar Imo da sauran jihohin inyamurai, Nnamdi Kanu yace musu bai son ganin jami'in tsaro ko guda daya a yankin
Onye Army, ya kara da cewa an yaudaresu da sunan suna yaki ne domin neman 'yanci alhali 'yan uwansu suke kashewa, yace ko sisi ba'a biyansu, dole suyi sata suyi garkuwa da mutane domin neman kudi, yace yayi farin ciki da aka kama Nnamdi Kanu, kuma Onye Army yana rokon Gwamnatin Nigeria ta masa afuwa, sannan ta hukunta Nnamdi Kanu
Jama'a ya kamata Gwamnatin Nigeria ta yiwa Onye Army kwamandan ESN afuwa tunda ya nemi a masa afuwa?
Allah Ka tabbatar mana da tsaro da zaman lafiya a Kasarmu Nigeria Amin
Comments
Post a Comment