TSARO: Jami'an Najeriya sun cafke wadanda ake zargin Yan bindiga ne guda 100
Jami'an tsaro sunyi dirai Mikiya a Kauyen Ramon yankin Dambuwa dake Karamar hukumar Shuni a Jahar Sokoto inda suka cafke Yan bindiga da ake zargi sama da mutane 100.
Kauyen Ramon, na daga cikin kauyukan da rashin tsaro yayi kamari, sannan ya kasance kauye mafi hatsari saboda abubuwan dake wakana a yankin.
Kauyen ya zama mafaka ga Yan ta'adda, karuwai, barayi, masu safarar kayan maye da made duk nau'in miyagun ayyuka.
Jami'an tsaron sun hada da Jami'an dake dakile safarar miyagun kwayoyi NDLEA, Jami'an NSCDC, Jami'an kwastom, Jami'an FRSC, Jami'an Yan sanda.
Jami'an dai sunyi dirar Mikiya ne a Kauyen da misalin karfe 5:00pm inda suka share awanni biyu suna bincike.
Wadanda Ake Zargin dai an tafi dasu zuwa shal kwatan Yan sanda dake Jahar Sokoto don cikaken bincike akan su.
Daya daga cikin manema labarai na Jaridar Dailytrust, lokacin da yaje shal kwatan don ganinma idansa yace cikin wadanda aka kama harda Mata.
ASP Sunusi Abubakar Mai magana da yawun Yan sanda ya tabbatar da anyi nasarar cafke mutane 144 wadanda ake zargin tare da miyagun kwayoyi.
Yace "Zamu bincike su sosai wànda muka tabbatar da laifinsa zai fuskanci hukunci daidai da abunda suka aikata."
Comments
Post a Comment