Min menu

Pages

Wasu kungiyoyi sun maka Buhari a kotu saboda wadannan dalilan

 Wasu kungiyoyi sun maka Buhari a kotu saboda wadannan dalilan




Kungiyar yarabawa ta Ilana Omo Oodua a Nijeriya, da wasu kungiyoyi 49 sun maka shugaba Muhammadu Buhari gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC inda suka gabartar da wasu takardun korafi mai shafuka 27.



Shugabanni da yawa na kungiyoyin kafa kasar Yarabawa ciki har da Farfesa Banji Akintoye, da Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ne suka rattaba hannu a takardun korafin wanda jaridun Nijeriya suka tabbatar.


Rahotanni daga kasar sun lura da cewa an gabatar da korafin gaban kotun ta ICC ne a madadin shugabannin wasu kungiyoyin Yarabawa ta hannun wani lauyan kasa-da-kasa mai suna Aderemilekun Omojola.


A cikin takardar karar, an zargi wasu shugabannin Najeriya da aikata kisan kare dangi, cin zarafin bil'adama akan al'ummar ta Yarbawa da ke jihohin Ekiti da Oyo da Osun da Ondo da Ogun da kuma garin Okun da ke jihar Kogi da Kwara.


Wadanda aka gurfanar a gaban kotun ta ICC sun hada da shugaba Muhammadu Buharin da Ministan Shari'a  Abubakar Malami kana tsohon shugaban hafsin sojin kasar Tukur Buratai da tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda, Ibrahim Idris da takwaransa Muhammad Adamu.


Takardar karar mai shafuka 27 ta zargi shugaba Buhari da Abubakar Malami da kuma Buratai da laifukan kisan kare dangi kan mambobin kungiyar masu shigar da karar hadi da jikkata wasu daga cikinsu da kuma haifar da firgici a zukatan mambobin masu rajin kafa kasar Yarabawan.


Tuni dai Kotun ta ICC a hukumance ta amince da karbar takardar korafin da aka shigar gabanta.

Comments