Wata kabila wacce basa binne yan uwansu idan sun mutu.
Assalamu alaikum barka da wannan lokaci sannunku da hakurin kasancewa damu a wannan gidan mai tarin albarka, hakika muna jin dadi yadda kuke ziyartar wannna gidan namu a koda yaushe.
Wannan abinda kuke mana yana matukar kara mana kwazo da jin dadi dan haka muke iya bincike mu zakulo muku abubuwa na mamaki da kuma na al'ajabi wanda muka san zai nishadantar daku.
Yau cikin hukuncin ubangiji munzo muku da labarin wata kabila wacce su idan dan uwansu ko yar uwarsu suka mutu basa binne su maimakon haka ma kusan komai tare suke yi kamar kwana ko zama.
Duk lokacin da wani ya mutu to su wadannan kabilun suna kula da gawar, sukan yiwa gawar wanka su tsayar da ita su saka mata kaya sannan su kawo abinci da abin sha suna dura mata duk da suna gani abincin baya tafiya.
Bayan sunyi wannan wasu ma daga cikinsu sukan kunnawa taba wuta sannan su bude bakin gawar su saka mata haka harta gama cinyewa ta mutu.
Bayan kayansu yayi datti sukan cire musu sannan su saka musu wani suje su wanke musu wadannan din.
Ada kabilar suna amfani da ganyen itatuwa domin su hana gawar baci a wancan lokacin to amma yanzu suna zuba musu chemical ne domin karsu baci.
Basa damuwa suna kwana daki daya dasu ba tare da wani damuwa ko jin tsoron wani abu ba.
Sudai wadannan kabilar acan kasar Indonesia suke kuma sunan kabilar tojara.
To jama'a anan zamu tsaya dan haka mu hadu a wani shirin da zamu kawo muku nan gaba kadan insha Allahu idan yayi muku kuyi mana comments domin mu gane mun gode sosai.
Comments
Post a Comment