Yadda DSS ta gano manyan bindigogi da alburusai a gidan jagoran 'yan a-waren Yarabawa
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta ce ta gano manyan bindigogi da alburusai a gidan mai rajin kare Yarabawan nan Sunday Igboho.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis, ta ce jami'anta ne suka kai sumame gidan Sunday Adeniyi Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho da ke Soka, a Ibadan da ke jihar Oyo.
Hukumar ta ce ta tura jami'an nata ne sakamakon samun bayanan sirri da ke nuna cewa ya tara makamai a gidan.
Sanarwar, mai dauke da sa hannun kakakin hukumar Peter Afunanya, ta ce lokacin da jami'an suka isa sai wasu mutane tara da take zargin masu gadin Igboho ne suka far musu dauke da bindigogi kirar AK-47 da kuma wasu uku da bindigogi kirar harbi-ka-ruga.
A yayin musayar wutar an bindige mutane biyu da aka tarar a gidan Igboho dauke da makamai yayin da kuma aka kama sauran", a cewar DSS.
DSS ta ce jami'inta daya ne kacal maharan suka harba a hannunsa na dama.
Ga wasu makamai da DSS tace ta kama a gidan.
Bindigogi kirar AK-47 guda bakwai
Bindigogi kirar harbi ka ruga Uku
Bindigogi kirar AK47 37 makare tam, da harsashi
Harsasai dubu biyar
zabga zabgan wukake 11.
Kananan bindigogin tafi da gidanka (Pistol) guda biyu.
Na'urar hange daga nesa daya.
Jaka, dauke da dalolin Amurka, da lasisin tuƙi na cikin gida da na waje, da katunan cirar kudi na ATM, da takardar izinin zama dan kasa ta Jamus mai lamba YO2N6K1NY mai ɗauke da sunansa;
Usur na busa guda biyu.
Abun nadar bayanai guda biyar.
Rediyon oba-oba guda biyar.
Rigunan ninja da dama.
Kwamfiyutoci kirar Laptop guda hudu.
Hukumar ta DSS ta ce baya ga dukkan wadannan kayayyaki da ta gano a gidan Sunday Igboho, ta kuma kama kimanin mutum goma sha uku da suka hada da maza sha biyu da mace daya, kuma tuni aka kai su Abuja.
DSS ta ce Sunday Igboho ya tsere
Ta ce lokacin da ake gwabza arangamar ne mutumin da ake magana Sunday Igboho ya tsallake ya guda
Hukumar tsaron farin kayan ta Najeriya ta ce ko a ranar Lahadi, Igboho da jama'arsa sun kitsa kai hari da sunan neman yancin kafa kasar Yarbawa, don haka a cewarta ''Wannan kame da ta yi tabbaci ne na wani babban shiri da mutumin da yaransa ke yi na tada zaune tsaye a Najeriya''.
A don haka ne take jan hankalin kasashen duniya bisa tunanin watakila zai iya neman sabunta takardun shaidarsa na zama a wata kasa bisa basu hujjar cewa sun bace.
DSS ta ce Sunday Igboho ya tsallake ya fice daga cikin gidan lokacinda jami'anta ke gwabzawa da yaransa.
Kazalika ta umarce shi da ya mika kansa don fuskantar bincike a kan laifukan da ake zarginsa da aikatawa.
Comments
Post a Comment