Min menu

Pages

Yanzu yanzu aka hangi Sunday Igboho na kokarin fita daga Nigeria>>Gwamnati ta ankarar da Jami'an tsaro dasu hanashi fita

 Sunday Igboho na kokarin fita daga Nigeria>>Gwamnati ta ankarar da Jami'an tsaro dasu hanashi fita




Hukumomin tsaro a Nigeria, sun ankarar da Shuwagabanni akan su tsayar da Dan Gwagwarmayar yarbawa Sunday Adeyemo, wanda akafi sani da Sunday Igboho daga fita daga Kasar.


A takardar da Hukumar kula da Shige da Fice ta Kasa ta sanar da Hukumar Yansanda, da Hukumar Jami'an tsaro ta Farin Kaya, da sauran Hukumomin tsaro cewa "an samu bayanan sirri cewa Adeyemo na kokarin samun takarda daga Yansanda da shaidar canja suna domin ya fita daga Kasar.


Hukumar kula da Shige da Fice tayi nuni dacewa, hakan zai taimakawa Igboho samun sabon Fasfo, dazai taimaka mashi ya fice daga Kasar."


Gwamnati tace tuni ta sanya sunan Sunday Igboho, a cikin sunaye wadanda ta hana fita daga Kasar, domin taimakawa wajen kama shi.


Gwamnati tace ta baiwa Jami'an tsaro umarnin kamo Igboho a duk inda aka same shi.


Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da Hukumar Shige da Fice ta Nigeria, ta sanar a ranar 9 ga watan Juli na Shekarar 2021, inda ta kaita ga Darakta-Janar na Hukumar Jami'an tsaro na Farin Kaya, da Sufeto-Janar na Yansanda da Darakta-Janar na Hukumar Sirri ta Kasa wato-NIA.


Hukumar Jami'an tsaro na Farin Kaya ta sanya Igboho, a cikin wanda take nema ruwa a jallo, sakamakon zargin sa ga mallakar makamai da ruguza kasa, Wanda ya tuni ya karyata hakan, amma kuma an neme shi an rasa.


Har yanzu an rasa inda Igboho yake, tun lokacin da aka kai hari a gidansa, Wanda Hukumar Jami'an tsaro na Farin Kaya suka yi da sauran Jami'an tsaro, inda aka kashe masu taimaka masa tare da tafiya da matarshi da sauran iyalansa.

Comments