Adam A Zango dai ya fadi abinda ya shiga tsakanin su da Ummi Rahab
A wata tattaunawa da Adam A Zango ya yi a yammacin ranar Alhamis 19 ga watan Agustan shekarar 2021, ya bawa masoyansa dama su masa tambayoyi a shafin sa na Instagram.
Fitaccen jarumin ya samu tambayoyi da dama daga wajen masoya kuma mabiyansa a shafin na sa na Instagram.
WATA SABUWA:-INA IYAYEN UMMI RAHAB ?
Tarihin Ummi Rahab da haduwar su da Zango
Sai dai wani ya masa tambaya kan dalilin cire Ummi Rahab daga cikin fim din sa na Farin Wata Sha Kallo, Adam A Zango ya bayyana masa cewa ba shine ya haifi Ummi Rahab ba, ya kara da cewa koda ma ace shine ya haifeta idan ya nuna mata hanya ta ki bi zai iya kyaleta ta yi abinda ta ga dama.
A karshe Adam A Zango ya roki Allah ya shirye ta ya kuma sa ta gane, kana ya kare da cewa duk wani da za a ganta ko a nan gaba kada a zarge shi, a zargi kamfanin da ta koma, ga dai yadda tattaunawar ta kasance da jarumin:
Lokacin da na fara fim din farin wata, rubutu na ne, kamfanina ne, fasaha ta ce, ba bu kudin kowa a ciki, na saka wanda nake so ba tare dana yi shawara da kowa ba. Hakazalika idan zan cire wani a ciki ai ba zan nemi shawarar kowa ba, saboda ni ina yin abinda na tabbatar ‘yan kallo za su kalla su ji dadi.
Na san ‘yan kallo za su so su ji dalilin da ya sanya muka cire ta, da ita Ummi Rahab da kuma Zahra ‘Yar Buzuwa, lokacin dana sanar cewa na canza su na sha zagi ta uwa ta uba, daga karshe kuma masu zagin suka ga cewa aure ta yi, to ban san ko so suke na sanar da mijinta cewa ya sake ta ba?
Ita kuma Ummi ina so ku fahimci cewa ni ina daukar fim da halin da masana’antar Kannywood ke ciki na karyewar kasuwa, saboda haka yadda abubuwa suke a da ba haka suke yanzu ba. Yanzu farfadowa muke muna shirin kawo muku wata hanya da za ku dinga kallon fina-finan mu ba tare da kunje kasuwa kun saya ba saboda duniyar ta canja.
Lokacin dana dawo da Ummi Rahab harkar fim, na tabbatar da cewa lokacin na sha zagi, wasu ma daga kasashen ketare suke kira akan a kamani, saboda na dauko yarinya zan lalata ta, duk da haka na jure na saka ta har ta kawo wannan matsayi.
Maganar gaskiya duk wanda yake kamfanina, ko kanina koma waye, ina so na ga idan na ce maka kayi nan ka gane cewa ba cutar da kai zanyi ba, abu ne wanda yafi alkhairi. Saboda haka idan nayi iya yina kaga cewa hakan bai yi maka ba, sai na ce to Allah ya kiyaye hanya.
Abinda nake so Ummi ta yi ba shi take so ba, ni kuma ba wai ni ne na haifeta ba, dan da ka haifa ma kana iya ce mishi ga abinda kake so ya yi ya ce a’a shi haka zai yi, kuma babu yadda ka iya sai dai kayi masa fatan alkhairi. Saboda haka ita ma ina yi mata addu’ar Allah ya shiryeta ya ganar da ita.
Ita diya ce a wurina, saboda haka ba zai yiwu ace ‘ya ta tayi mini laifi sai na fito na fara sanarwa da duniya abinda ta yi mini ba, bazan kuma fadi abinda zai saka mutane za su fara yawo su ce za su zage ta ba. A karshe abinda nake so ku sani ko da wani abu zai je ya dawo kada ku ga laifina ko na kamfanina, ku dora laifin kamfanin da take aiki a ciki yanzu.
Magana daga bakin me ita dan haka ku saurari abinda yace
Comments
Post a Comment