Min menu

Pages

Aisha Buhari Cup: Anfitar da Rukunin A da B Tsakanin Ƙasashen Afrika

 Aisha Buhari Cup: Anfitar da Rukunin A da B Tsakanin Ƙasashen Afrika



An fitar da rukunin A da B na gasar cin kofin uwar gidan shugaban ƙasar Najeriya wato Hajiya Aisha Buhari gasar da akayimata laƙabi da Aisha Buhari Cup 2021.


An fitar da rukunan a wannan rana ta Laraba a Australian Hall Hotel tsakanin jerin ƙasashe guda 6.


Ga yadda aka fitar da rukunan:


Rukunin A akwai ƙungiyar ƙwallon ƙafan mata ta Najeriya wato Super Falcons da Morocco da kuma ƙasar Mali.


Rukunin B akwai Cameroon da Black Queens wato Ghana da kuma Afrika ta Kudu.


Shugabar Hukumar dake shirya gasar cin kofin premier ta mata ta ƙasar Najeriya wato Aisha Folade ta jagoranci raba rukunin dare da jagorar 'yanwasan ƙungiyar ƙwallon ƙafan mata ta F/C Robo Queens da ake kira da Monday Gift suka jagoranci raba rukunin da  kuma sauran wasu mutanen.


Za a fara fafata gasar a ranar 13 ga watan gobe na Satumba, 2021. Sannan za a fafata wasannin gasar a santoci guda biyu wato Mabolaji Johnson Arena, Onikan da Teslim Balogun, Surulere dage Lagos.


An bayyana cewar za a bi matakan kariya sosai tun daga ƙpfar shiga sabo da cutar nan da take yawo a Najeriya wato Corona Virus.

Comments