DA GASKE TALIBAN YAN TA'ADDA NE? Duk wani musulmi ya kamata yasan wannan
TALIBAN ‘YAN TA’ADDA NE?
Ina so don girman Allah duk wani Musulmi da zai soki kungiyar Taliban ya lika mata ta’addanci to yayi bincike mai zurfi zai fahimci gaskiya, Amerika da Ingila da sauran kasashen yahudu da nasara sun gurbata kalma da hanyoyin jihadi ta hanyar daukar nauyin wasu gurbatattun Musulmi, aka wayi gari ana kallon duk wata kungiya na Musulmi da take jihadi a matsayin ta’addanci
Kafin shekarar 1980s babu wata kungiya na Musulmi da ta dauki makami take yaki da sunan ta’addanci, babu wata kungiya a duniya da aka lakaba mata sunan kungiyar ‘yan ta’adda
A lokacin da tsohuwar tarayya Soviet wato Kasar Russia a yanzu ta tashi mamayar Kasar Afghanistan a shekarar 1979, kungiyar Taliban, kungiyar Alq’idah da na shi’ah da ‘yan ikhwan da sauran kungiyoyin Musulmi da taimakon Amerika da Saudiyyah sun hadu guri guda, Amerika ta bada horon soji da kayan yaki aka hadu aka yaki Soviet, an samu nasaran fatattakar Soviet daga Afghanistan a karshen shekaran 1990
Bayan kammala wannan yakin, tsohon shugaban Kasar Amerika na lokacin Mr Ronald Reagan ya kira su Osama bin Laden har zuwa fadar White House ya karramasu ya yabesu a idon duniya, a lokacin sai sauran kungiyoyin Musulmi irinsu Alqa’ida suka cigaba da rike makami da sunan zasuyi jihadin tabbatar da shari’ar Musulunci a doron kasa
Idan mun lura, duk bayan shekaru 10 (decade) sai wani abu ya faru a duniya, anyi shekaru 10 ana yaki da Soviet a Afghanistan, bayan wata shekara 10 da aka kori Soviet, sai aka wayi gari an kaddamar da mummunan harin ta’addanci a cibiyar Kasuwanci na duniya (World Trade Center) dake birnin Washington na Amurka, inda aka hallaka dubbannin mutane a lokaci guda
Gwamnatin Amerika karkashin jagorancin George W. Bush ta daura alhakkin harin akan kungiyar Alq’idah ta su Osama bin Laden, ta hanyar amfani da jirgin fasinjoji na Amurka wanda Amurka tace ‘yan Alqa’ida ne suka yiwa jirgin kutse suka bugi tagwayen ginin cibiyar Kasuwanci na duniya, harin ya faru a ranar 11 ga watan 9 na shekarar 2001, a lokacin DA harin ya faru kungiyar Taliban itace take mulki a Kasar Afghanistan, sai Amerika ta bukaci Taliban ta mika mata Osama bin Laden domin ta hukuntashi, sai Gwamnatin Taliban taki amincewa
Watanni uku da harin, jirgin farko na sojojin kundunbala na Kasar Amerika a ranar 7 ga watan 12 na shekarar 2001 sun sauka a doron Kasar Afghanistan da nufin yakar kungiyar Alq’idah na su Osama bin Laden, sai dai a lokacin akwai manyan ‘yan siyasar Amerika wadanda suke ganin babu hujjar da Amerika zata yaki Afghanistan, hatta shugaban Amerika na yanzu Joe Biden lokacin yana Sanata, yana daga cikin wadanda suka soki burin Amerika na yakar Afghanistan
Kungiyar Taliban ta kafa Gwamnati a Kasar Afghanistan a shekarar 1996 kafin Amerika ta kifar da Gwamnatinta ta hanyar zalunci a 2001, babban abinda da ya kamata a fahimta, idan akwai kungiyar da tafi kusa da ta’addanci a Afghanistan to bai wuce kungiyar Alq’ida ba, Alqa’ida kuwa kirkiran CIA na Amurka ne, Taliban ta yaki Alqa’ida, Taliban bata da alaka ko kusa da kungiyar Alq’idah, abinda Taliban ta saka a gaba shine ayi shari’ah abi dokar Allah (T), laifin Taliban a gurin Amerika shine taki mika Osama ga Amerika
Ina so jama’a su fahimci wani abu, idan zalunci yayi yawa akan wasu kebantattun mutane da ake yakar gurbatattun cikinsu ana taba wadanda basu ji ba basu gani ba, to hakan yana jawo mutane kowa da kowa su dauki makami su zama azzaluman dole, shigen irin abinda ya faru da fulanin jeji anan Arewacin Nigeria kenan da suke garkuwa da mutane, zaluncin wasu gurbatattun jami’an tsaro ya jawo haka, farkon al’amari idan jami’an tsaro sun shiga jeji farautar barayin shanu, duk makiyayi da aka gani akan hanya sai a harbeshi a kora shanunsa a aure matarsa, wannan zaluncin na daga cikin abinda ya jefa mu cikin bala’i na kidnapping a yau
Shigen irin wannan zalunci Amerika tayi a Kasar Afghanistan, ita kuma a tsarin Amerika shine duk wata kungiya na Musulmi da ta tashi tana Gwagwarmaya tare da sukar tsarin mulkin Demokaradiyyah, to Amerika zata dauki wannan kungiyar a matsayin kungiyar ta’addanci, tayi amfani da manyan kafofin watsa labaranta wajen yada batanci da sharri akanta domin ta gamsar da duniya hujjar da zata yaki wannan kungiya na Musulunci
Lokacin da Amerika ta shiga Afghanistan domin ta yaki Alqa’ida, ta tarar ana shari’ar Musulunci 100 bisa 100 a Afghanistan karkashin Gwamnatin Taliban, amma bayan Amerika ta kaddamar da hari a Kasar Afghanistan da zummar zata yaki kungiyar Alq’ida, Amerika ta fake da wannan ta aikata mummunan zalunci da cin zarafin Musulmi maza da mata, amma da yake sune da media basa bari a zayyana
Kafin Amerika ta fice daga Afghanistan sai da ta kawo barna da fasadi a Kasar, ta samar da gidan giya, ta samar da gidan karuwai, ta koyawa matasa maza da mata lalata da Luwadi da shaye-shayen miyagun kwayoyi, wanda dama wannan shine babbar manufar ta na shiga Kasar Afghanistan domin ta rusa Musulunci da shari’ah ba don wai ta dauki fansar harin 11/9 ba
Zan so jama’a su nemi wata Lecture da Marigayi Sheikh Albaniy Zaria yayi mai taken MUNAFURCI DODO NE yayi kaset har uku, to ku nemi kaset na ukun, Malam ya tona asirin makircin Amerika akan harin 11/9, Malam yace Amerika ne ta kitsa abinta saboa ta cimma manyan bukatu uku zuwa hudu, 1- domin ta sace kudin kasashen duniya, 2- domin ta likawa Musulmi kalmar ta’addanci, 3- domin ta samu hujjar shiga kasashen Musulmi ta rusa Gwamnatin Musulunci ta dasa tsarin mulkin Demokaradiyyah
Ta ina aka ce Taliban ‘yan ta’adda ne? amsa, ta kafofin watsa labaran yahudu da nasara, kafin bayyanar wayar salula da kafofin watsa labarai na yanar gizo, kamar mu anan Nigeria, gaba dayanmu mun ta’allaka ne akan sauraron labari kan abinda yake faruwa a kasashen Musulmi daga manyan kafofin watsa labarai na yahudu da nasara makiya Musulunci irinsu BBC, DW, VOA, CNN da sauran jaridu wadanda ba na Musulmi ba
Musulmi an yi mana yakin kwakwalwa (Phsycological War) an saka mana tsoro ta hanyoyin farfaganda da karya, an gurbata tunanin mu, yahudawa sun yada karya da batanci ta kafofin watsa labaransu da muke saurare, kuma yayi tasiri sosai a cikin zukatan mu, wanda har mun kai matsayin da idan labari ba daga BBC ko DW ko VOA da sauransu ba to ba za’a yadda ba, amma tabbas makaryata ne, lokacin muna yara, idan kaji ana yiwa mutum lakabi da BBC to tantirin makaryaci ne
Tun bayan shekarar 2001 duk wata kungiyar jihadi da ta bayyana a duniyar yau idan an bincika sai an tarar Amerika tana da hannu wajen kafata da kuma tallafa mata da kayan yaki domin ta yaki Musulmi, shiyasa kuka ga jihadin kungiyoyin ta’addanci baya karewa akan kowa sai Musulmai, kungiya mafi muni da tayi ta’addanci a baya bayan nan itace ISIS, manyan Kwamandadojin yakin ISIS su Abubakar Al-baghdadi da Jihadi John duka jami’an CIA ne na Amurka, Taliban ta yaki ISIS da duk dukkan rassanta, saboda, zalunci da ta’addanci bayan cikin tsarin Taliban
A cikin Gwagwarmayar Taliban ba za’a taba rabasu da wasu kurakurai ba, amma duk wanda ya jingina musu ta’addanci to ya zaluncesu, kuma ya tanadi hujjar da zai kare kansa ranar Hisabi, mutanene wanda abinda suka saka a gaba shine abi Allah kawai, a dawo da shari’a, mata su saka hijabi, maza su bar gemu, a raba cakuduwa tsakanin maza da mata, a dena sayar da giya da miyagun kwayoyi
A tsarin Gwagwarmayar Taliban basa kashe mata da kananan yara da duk wanda bai yake su ba, gwagwarmaya suke na neman ‘yanta addinin Allah daga cutarwan tsarin mulkin Demokaradiyyah, kuma duk garin da suka karba cewa suke a zauna lafiya, abi Allah, basa kunar bakin wake, basa kashe mutanen da Allah Ya haramta a kashe, kuskuren su bai wuce zafafawa da suke da kuma saka dokokin Gwamnati masu tsauri ba
Bayan shekaru 20 cif da aka kwace Gwamnatin Taliban a Afghanistan, yau Allah Ya basu nasaran karban mulkin su, Insha Allahu muna kyautata wa Taliban zato na alheri shari’ar Musulunci zai dawo a Afghanistan, zaman lafiya da kwanciyar hankali zai dawo
Allah Ka daukaka Musulunci da Musulmai a duk inda suke Amin
Comments
Post a Comment