JIGO A JAMIYYAR APC YA TAFI KOTU DOMIN NEMA MA BUHARI DAMAR TSAWA TAKARA KARO NA UKU.
Jigo a jamiyyar APC Charles Oko Enya, ya shigar da kara a kotu, yana so a ba gwamnoni da kuma shugaban kasa damar yin wa’adi uku a ofis.
Shi dai Oko Enya, ya kai karar majalisar tarayya da ministan shari’a na kasa, a babban kotun tarayya da ke Abakaliki, jihar Ebonyi.
Dan siyasar yana so kotu ta yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima ta yadda za a cire takunkumin da aka sa wa masu mulki na yin wa’adi biyu.
A cewar Oko Enya, babu adalci idan ‘yan majalisa za su iya takara har sai sun gaji, amma shugaban kasa da gwamnonin ba su iya wuce shekara takwas.
Rihoton ya tabbatar da cewa Barista Agboti Iheanacho shi ne babban lauyan da zai tsaya wa jigon na jam’iyyar APC a gaban Alkali. Domin jin bukatar sa.
Abinda ya dogaro da shi shi ne - :
Takardun da aka gani a ranar Laraba, 18 ga watan Agusta, 2021, sun nuna Lauyan yana cewa sashe na 137(1)(b) ya takaita burin gwamnoni da shugaban kasa. Agboti Iheanacho yake cewa wannan sashe da ya kayyade wa’adi biyu na shekaru hudu bai da hurumin zama a tsarin mulkin kasa saboda ba ayi adalci ba.
Iheanacho ya roki kotu ta umarci Ministan shari’a, kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, ya yi wa sashe na 127 na kundin tsarin mulkin Nijeriya kasar garambawul. Domin shugaban kasa ya samu Zarafin yin wa'adi na uku tare da Gwamnoni.
Yanzu dai Alkali yace zai saurari karar Charles Enya wanda ya yi wa jam’iyyar APC shugaban yakin neman zabe a jihar Ebonyi a zaben 2019 nan da makonni biyu masu zuwa domin duba bukatar nasa
Ko me za kuce kan wannan ra'ayi na Charles Oko Enya,...?
Comments
Post a Comment