Min menu

Pages

LABARI DA ƊUMI ƊUMIN SA! Kwana daya da ziyartar shugaban sojoji jihar zamfara dubi abinda ya faru

 LABARI DA ƊUMI ƊUMIN SA! Kwana daya da ziyartar shugaban sojoji jihar zamfara dubi abinda ya faru



Kwana daya da ziyarar shugaban Hafsan sojin Najeriya Janar Farouk Yahaya a jihar Zamfara, sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 78 a jihar Zamfara ta hanyar yi misu ruwan boma-bomai


Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce jiragen yakinta sun yi luguden bama-bamai a kan sansanonin 'yan fashin daji na jihar Zamfara - har ma sun kashe aƙalla saba'in da takwas daga cikin su.


A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar, sojojin saman na Najeriya sun ce wasu daga cikin 'yan fashin dajin kuma sun tsere yayin samamen.


Ta ce hadin gwiwar dakarun tsaron sun kwashe tsawon kwana uku tun daga ranar Litinin har zuwa Laraba suna lugude a kan 'yan fashin dajin - waɗanda suka addabi yankin.


A cewar rundunar luguden bama-baman ya shafi sansanonin 'yan fashin dajin da ke cikin dajin Kuyanbana, kudu da garin Ɗan Sadau dake cikin ƙaramar hukumar Maru.


Zamfara dai na daga cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren 'yan fashin daji a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, waɗanda ke cin karensu babu babbaka a sassa da dama na jihohin Neja da Zamfara da Kaduna da Sokoto da Katsina da kuma Kebbi.


Rundunar sojin saman Najeriya dai ta ce yayin wannan artabun sojoji na kwana uku, an yi amfani da jiragen yaƙi iri daban-daban don tarwatsa sansanonin 'yan bindigar.


Ta ce wasu daga cikin 'yan fashin dajin ma, an kashe su ne a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa a kan babura, duk da yake, akwai wasu a cikinsu da suka tseren.


Haka zalika, an lalata sansanoni da dama na 'yan fashin daji da ke cikin dajin na Kuyanbana, a cewar rundunar sojin saman Najeriya kamar yanda bbc suka wallafa.


Sojojin sun kuma ce a wani lokaci sai da aka yi amfani da tallafin sojojin ƙasan Najeriya wajen yi wa 'yan bindigar ƙofar rago da kuma datse hanyoyinsu na tserewa.


Samamen dai ana iya cewa shi ne na baya-bayan nan da haɗin gwiwar sojojin sama da na ƙasan Najeriya ke kai wa don murƙushe ɓarayin dajin a shiyyar arewa maso yamma.

Comments